Yayin da yara a duniya da Isra'ila ke komawa makaranta, na Gaza kuwa ana ci gaba da kashe su

Yayin da yara a duniya da Isra'ila ke komawa makaranta, na Gaza kuwa ana ci gaba da kashe su

Sojojin Isra'ila sun kashe dalibai sama da 10,000 tare da raba dubu 19 da muhallansu tare da lalata daruruwan makarantu a Gaza.
A wannan shekara Isra'ila ta shirya don ɗaukar ɗalibai sama da miliyan 2.5 a duk faɗin ƙasar. [TRT World]

Yayin da dalibai a Isra'ila suka fara sabuwar shekarar karatunsu da sabbin jakunkuna da litattafai, da kayan rubutu a ranar Litinin, yara a Gaza na fuskantar wani lamari na daban, inda da yawa ko dai sun mutu ko kuma makarantunsu sun zama baraguzai.

A wannan shekara Isra'ila ta shirya don ɗaukar ɗalibai sama da miliyan 2.5 a duk faɗin ƙasar.

Wannan ya hada da yara 'yan nazire 535,000 da ɗaliban babbar sakandare 514,000 da na ƙaramar sakandare 335,000, da na firamare 1,174,000, a cewar kafafen yada labaran Isra’ila.

Ga kasa mai miliyan tara, tana da ma'aikatan ilimi masu yawa, waɗanda suka ƙunshi ma'aikata 236,000 da shugabanni 5,754, da malamai sama da 200,000.

Amma ba a sami jawaban maraba ba kai ko da runguma mai sa hawaye daga iyaye a ƙofofin makarantu, ko sabbin kayan makaranta ko jakunkuna ga yaran Falasɗinawa a Gaza, inda har yanzu karatu ya tsaya cik saboda ci gaba da kai hare-hare da Isra'ila ke yi wanda ya fara a ranar 7 ga Oktoban 2023.

Sama da dalibai 10,000 ne aka kashe a Gaza tare da jikkata wasu 15,000 sakamakon hare-haren da Isra’ila ke kaiwa, inda dalibai 19,000 suka rasa matsugunansu, kamar yadda Ma’aikatar Ilimi ta Falasdinu ta bayyana.

Isra'ila ta kuma kashe akalla malamai 400 tare da lalata kashi 90 na gine-ginen makarantu a Gaza. Kimanin yara Falasdinawan 58,000 ne aka hana su zuwa matakin farko, matakin da ya dace a tafiyar ilimi.

Kusan Falasdinawa 41,000 - akasari mata da yara - aka kashe a wadannan hare-haren kuma kusan 95,000 sun sami raunuka, a ƙiyasin masu ra'ayin mazan jiya.

Bahaa da Batool, daliban makarantar sakandare masu shekaru 17 a Gaza, kamar sauran manyan makarantun sakandare 89,000 a Falasdinu, suna shirye-shiryen yin jarrabawar shiga jami'a, wadda aka fi sani da Tawjihi.

Amma yakin kisan kare dangi na Isra'ila ya hana Bahaa da wasu dalibai kusan 39,000 a Gaza cin jarrabawar da kuma ci gaba da neman cikar burinsu.

“Abin takaici, bayan yakin, sai aka koma kan yadda ake neman ruwa, a tara itace don a rura wuta a gasa burodi,” Bahaa ta shaida wa TRT World.

Tun daga watan Oktoba, akalla yara 625,000 a Gaza ba sa zuwa makaranta saboda yakin.

"Na yi fatan yin karatun likitan hakori a Jami'ar Al-Azhar. Yanzu, ina cikin sansanin 'yan gudun hijira a Deir al Balah," Batool Abualatta ta shaida wa TRT World.

Hare-haren wuce gona da iri kan ababen more rayuwa na ilimi na Gaza ya haifar da barna kai tsaye tare da raba yara da burikan makomarsu, wanda ya nakasa su, da barin su da rauni da rashin samun damar koyo.

A farkon watan Mayu, wani bincike da tauraron dan'adam ya gudanar ya nuna cewa kashi 85.8 na makarantu a Gaza, ciki har da na Majalisar Dinkin Duniya, sun lalace a wani bangare ko gaba daya sakamakon hare-haren da Isra'ila ta shafe watanni tana yi.

Mona Mohammed Abu Aida, mahaifiyar wani dalibin makaranta mai suna Hamoud ta ce "Ga mutane irinmu da har yanzu suke matsuguni a makarantu idan aka fara sabuwar shekarar karatu, wannan zai kasance shekara ta biyu da suka yi rashin nasara."

"Ina za mu je? Ina mutanen da ke cikin makarantun nan za su je?"

TRT World