Litinin, 2 ga watan Satumba, 2024
0955 GMT — Yawan Falasɗinawan da Isra;ila ta kashe a Gaza ya kai 40,786
Ma'aikatar Lafita ta Zirin Gaza ta ce aƙalla Falasɗinwa 40,786 aka kashe a hare-haren Isra'ila tare da jikkata wasu 94,224 tun fara yaƙinta a Gaza ranar 7 ga watan Oktoban bara.
0750 GMT — Firaministan Malaysia Anwar Ibrahim da takwaransa na New Zealand Chris Luxon sun ce sun haɗa kai wajen kira a yi gaggawar tsagaita wuta a kisan kiyashin da Isra'ila ta kwashe wata 11 tana yi a Gaza tare da kafa ƙasase biyu - na Israila da Falasɗinu - masu 'yancin kansu.
"Dukanmu mun haɗa kai wajen yin kira a gaggauta tsagaita wuta, sannan ɓangarorin biyu su hau teburin sulhu kana a samar da ƙasashe biyu masu 'yancin kansu," kamar yadda Luxon ya sanar a taron manema labarai da suka gudanar.
Luxon ya je Malaysia ne domin yin ziyarar aiki ta kwana uku.
Anwar ya ce a halin da ake ciki ba su ga wata alama da ke nuna cewa za a tsagaita wuta ba, yana mai ƙari da cewa ƙasashe irinsu Amurka ba sa matsa lamba don tsagaita wuta kamar yadda ya kamata.
0123 GMT —Isra'ila ta jefa bama-bamai a gidajen jama'a a Gaza, ta kashe Falasɗinawa
Dakarun Isra'ila sun kashe fararen-hula biyu tare da jikkata wasu bayan sun jefa bama-bamai a wani gida da ke arewa maso yammacin Birnin Gaza, a cewar kamfanin dillancin labarai na Falasɗinu WAFA.
Rundunar kare fararen-hula ta yankin ta ce ta ɗauko gawa biyu da kuma mutanen da suka jikkata daga gidan iyalan Araj da ke Jalaa Street bayan Isra'ila ta kashe su.
Daga bisani adadin mutanen da suka mutu ya ƙaru zuwa 11 bayan jiragen yaƙin Isra'ila sun kai hari a Makarantar Safad da ke kudu maso gabashin Gaza, inda 'yan gudun hijira suke fakewa.
Ma'aikatan ceto sun ci gaba da gudanar da aikin tono wasu mutanen da suka maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine, yayin da Isra'ila ke barazanar ci gaba da kai hare-hare a yankin.
0109 GMT — Ministan harkokin wajen Saudiyya na yunƙurin ganin an daina kai hare-hare a Gaza
Ministan harkokin wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan ya tattauna ta wayar tarho da takwarorinsa na Turkiyya, Masar, Jordan, Bahrain da Gambia ranar Lahadi a yunƙurin ganin Isra'ila ta daina kai hare-hare a Gaza da kuma bai wa Falasɗinawa 'yanci.
Bin Farhan ya yi magana da Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan game da bayanai na baya-bayan nan halin da Falasɗinawa suke ciki, inda ya mayar da hankali kan yunƙurin ƙasashen Musulmai na ganin sun maido da martabar Falasɗinawa da kuma haɗa-kai don kawo ƙarshen hare-hare da keta hakkin da Isra'ila take yi wa Falasɗinawa.
Da yake tattaunawa da Ministan Harkokin Wajen Masar Badr Abdelatty, ya mayar da hankali kan halin da yankunan Falasɗinawa suke ciki da kuma buƙatar ɗaukar matakan gaggawa domin dakatar da rashin mutuncin da Isra'ila take yi wa Falasɗinawa, yayin da kuma ya jaddada buƙatar samar da ƙasar Falasɗinu mai cin gashin kanta.
Kazalika a yayin da yake magana da Ministan Harkokin Wajen Jordan Ayman Safadi ya bayyana buƙatar gagauta tsagaita wuta da kuma haɗin-kan dukkan ƙasashen Larabawa da na Musulmai wajen ganin an yi wa Falasɗinawa adalci, ciki har da ƙirƙiro musu ƙasa mai cin gashin kanta.