Yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra'ila ta ƙulla da Lebanon ta soma aiki a yayin da al'ummar yankin Gabas ta Tsakiya, waɗanda ke cikin mawuyacin hali, suke ɗari-ɗari game da ɗorewarta.
Yarjejeniyar ta soma aiki da misalin ƙarfe 4 na safiyar Laraba, awanni bayan Isra'ila ta ƙaddamar da mummunan luguden wuta ta sama a babban birnin ƙasar wato Beirut. Isra'ila ta ƙaddamar da yaƙi a Lebanon tun watan Oktoban 2023.
Mazauna Beirut sun riƙa bukukuwa na murnar aiwatar da wannan yarjejeniya kuma babu wasu rahotanni na ƙin yin biyayya ga yarjejeniyar tun da aka tsagaita wuta.
Yarjejeniyar tsagaita wutar wadda aka sanar da ita ranar Talata wani babban ci gaba ne wajen kawo ƙarshen yaƙin kusan watanni 14 da aka fafata — inda Isra'ila ta kashe kusan mutum 4,000 da jikkata fiye da mutum 16,000 kana da raba mutum fiye da miliyan ɗaya da gidajensu a Lebanon — baya ga ta'azzara yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza.
A ɓangare guda, mayaƙan Hezbollah sun kashe sojojin Israi'la aƙalla 82 da fararen-hula 47, a cewar hukumomi.
Isra'ila ta ce za ta kai hare-hare muddun ƙungiyar Hezbollah ta karya yarjejeniyar. Kawo yanzu Hezbollah ba ta ce komai ba game da lamarin.