Zanga-zangar nuna rashin jin dadi kan kona Alkur'ani. Hoto: AP Archive    

Adadin 'yan kasar Sweden da ke son a haramta kona Alkur'ani da sauran littafai masu tsarki ya kai kaso 53 cikin 100, wato an samu karin kaso biyu kenan.

Wani kamfanin Sweden mai suna SIFO shi ne ya shirya kuri'ar jin ra'ayin jama'a kan wannan batun.

Akwai kaso 37 cikin 100 na 'yan Sweden da ke goyon bayan kona Alkur'ani karkashin dokar 'yancin fadin albarkacin baki, yayin wasu daga cikin 'yan kasar ba su bayyana ra'ayinsu ba.

An yi amfani da mutum 1,291 'yan Sweden wajen gudanar da kuri'ar jin ra'ayin jama'a tsakanin 15 zuwa 27 ga watan Agusta.

Gwamnati da babbar jam'iyyar hamayyar Sweden suna shirin canja dokar da ke bayar da damar kona Alkur'ani.

Tun da farko a watan jiya gwamnatin Sweden ta sanar cewa tana sake nazari kan Dokar Tabbatar da Kwanciyar Hankali ta yadda za ta hana wulakanta Alkur'ani a kasar.

Labari mai alaka: Sweden ta bari ana ci gaba da kona Alkur'ani yayin da ake takaddama kan shigarta NATO

Ministan Shari'a Gunnar Strommer ya bayyana yayin ganawa da manema labarai wani rahoto kan dokar wanda za a mika wa majalisar dokokin kasar a ranar 1 ga watan Yulin shekarar 2024.

Shugabar babbar jam'iyyar hamayya Social Democratic Party Magdalena Andersson ta ce suna bincike kan gyara Dokar Tabbatar da Kwanciyar Hankali, inda ta ce takalar da kona Alkur'ani ke jawowa za ta iya zama "laifin nuna kiyayya".

Denmark za ta yi doka

Ministan Shari'ar kasar Denmark Peter Hummelgaard ya bayyana yayin da yake ganawa da manema labarai a makon jiya cewa suna gab da yin kudirin doka kan wulakanta littafai masu tsarki.

Hummelgaard ya ce babban dalilin da ya sa ake wulakanta littafai masu tsarki shi ne "don jawo kiyayya da rashin jituwa" kuma kudirin dokar zai hada har da haramta kona tutar kasashe.

"Dokar za ta hukunta wadanda suka kona Alkur'ani da littafin Baibul a bainar jama'a. Dokar za ta kuma sanya ido kan abubuwan da aka yi a bainar jama'a da niyyar yada su zuwa cikin al'umma."

Ana saran gabatar da kudirin ne a watan Satumba ga majalisar dokoki mai mambobi 179 kuma a kada kuri'a a watan Oktoba bayan tuntubar majalisar.

A baya-bayan nan ana ci gaba da wulakanta Alkur'ani a Sweden da Denmark, abin da ke jawo suka da fushi a fadin duniya.

AA