1605 GMT — MDD ta koka kan zaluncin da sojojin Isra'ila ke yi kan wadanda ke tsare
Hukumar Kare Hakkin Bil’adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa ta samu bayanai masu tayar da hankali game da yadda sojojin Isra’ila ke kama mutane sannan tana azabtar da su a Gaza.
Kamar yadda rahotannin da aka samu daga ofishin Majalisar Dinkin Duniya ya nuna, “yara da ba su wuce shekara 12 ba da kuma tsofaffi wadanda suka kai shekara 70 na daga cikin wadanda sojojin suka tsare”.
Akasarin wadanda ake tsare da su din ana azabtar da su da kuma cin mutuncinsu.
1420 GMT — 'Yan jarida 92 Isra'ila ta kashe a Gaza tun daga 7 ga watan Oktoba
Akalla 'yan jarida 92 Isra'ila ta kashe a hare-haren da take kaiwa a Gaza tun daga 7 ga watan Oktoba, kamar yadda ofishin watsa labarai na Falasdinu ya tabbatar.
A wata sanarwa da ya fitar, ya ce 'yan jarida na baya-bayan nan da aka kashe sun hada da Rami Badir da Assem Kamal Musa wadanda aka kashe a lokacin da Isra'ila ta kai wani samame kwanaki biyu da suka gabata.
Ofishin bai yi karin bayani kan yadda aka kashe 'yan jaridar ba.
1155 GMT — Isra'ila ta kara kama Falasdinawa 20 a Gabar Yamma da Kogin Jordan
Sojojin Isra'ila sun kama karin Falasdinawa 20 a Gabar Yamma da Kogin Jordan a ranar Lahadi a samamen da Isra'ilan ke ci gaba da kaiwa.
Zuwa yanzu, adadin Falasdinawan da Isra'ilar ta kama a sun kai 4,4560 tun daga 7 ga watan Oktoba.
A wata sanarwa ta hadin gwiwa wadda hukumar da ke kula da sha'anin fursunoni da tsaffin fursunoni da kuma kungiyar Fursunoni ta Falasdinu, akasarin wadanda aka kama an kama su ne a Hebron da Bethlehem da Ramallah da Nablus da Tulkarim da ke Gabar Yamma da Kogin Jordan.
1056 GMT — Isra'ila ta kashe Falasdinawa 47 a safiyar Lahadi, daga ciki har da 'yan gudun hijira
Falasdinawa akalla 47 aka bayar da rahoton cewa Isra’ila ta kashe a wasu hare-haren sama da aka kai a birnin Jabalia da sansanin ‘yan gudun hijira na Deir Al-Balah a Zirin Gaza, kamar yadda kafar watsa labaran Falasdinu ta ruwaito.
“Falasdinawa 35 aka kashe gommai kuma suka samu rauni a ranar Lahadi a lokacin da Isra’ila ta tayar da bam a wani gida da ke birnin Jabalia a arewacin Zirin Gaza,” kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Falasdinu ya ruwaito.
Wasu mazauna yankunan sun tabbatar da cewa akwai wasu mutum 90 wadanda aka raunata wasu kuma na karkashin baraguzai.
"Jirigin yakin Isra'ila ya kuma kai hari wani gida da ke sansanin 'yan gudun hijira na Deir al-Balah wanda ke a tsakiyar Zirin Gaza, inda ya halaka akalla mutum 12 da raunata gommai, wadanda akasarinsu jama'ar da a baya suka rasa muhallansu ne," kamar yadda hukumar ta bayyana.