'Yan majalisar dokoki na Jam'iyyar Democrat a Michigan sun gargadi Fadar White House cewa yadda Shugaba Biden yake nuna halayya kan rikicin Zirin Gaza da hare-haren bam din Isra'ila bayan harin da Hamas ta kai zai iya janyo masa asarar kuri'un Musulmai Larabawa da ke kasar a zaben 2024, kuma jiha ce da yake bukatar ƙuri'unta don samun nasara.
Wannan lamari ya ja hankalin Fadar White House inda ta fara tattauna yadda za ta lalubo hanyar rage tashin hankalin tare da wasu jagororin Democrat na jihar, da suka hada da wasu da dama da suka yi shuhura wajen sukar Biden game da yaƙin.
"An isar da saƙon. Mun samu kiran wayoyi tare da White House. Mun yi waya da jami'an DNC," in ji Abraham Aiyash, ɗan jam'iyyar Democrat mai matsayi na uku a Majalisar Wakilai, wanda yake jagorantar Kwamitin Kasa na Democrat.
”Mun yi bayani ƙarara kan cewa dole ne a damu da insaniyya, amma idan wannan ba ya cikin lissafin da za ku yi a yanzu, to ku sani lallai za a samu targaden masu jefa kuri'a saboda hakan."
Michigan na da matukar mihimmanci, kuma tana cikin jihohin da suka hada da Wisconsin da Pennsylvania da ake yi wa laƙabi da shudin bango da Biden ya dawo da su Democrat, inda suka taimaka masa wajen shiga Fadar White House a 2020.
Tun wannan lokacin, 'yan Democrat suke samun kwarin gwiwa game da matsayinsu a Michigan, musamman bayan Gwamna Gretchen Whitmer ya samu maki goma a zaben da aka sake gudanarwa na rabin zango a bara.
Ba Trump ba Biden
Amma wasu abubuwa da suka faru a 'yan watannin nan sun jarraba ƙarfin jam'iyyar. Baya ga yakin, an samu rikici a Michigan tsakanin kungiyar ma'aikatan ƙera motoci da kamfanonin ƙera motoci uku da ke Detroit.
Tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ziyarci jihar a yayin yajin aikin da aka yi, kuma Biden da yake da alaƙa da ƙungiyoyin ya zama shugaba mai ci na farko da ya bi sahun masu yajin aikin.
A yanzu da aka warware matsalar, yakin na iya zama mai dogon tasiri na siyasa ga shugaban kasa. A 2020, Musulmai masu jefa kuri'a sun goyi bayan Biden, inda ya samu kaso 65, sai Trump d aya samu kaso 35 na kuri'un da aka jefa, kamar yadda alkaluman zabe na AP suka fitar.
Alyash, shugaban 'yan Democrat a fadar gwamnati, ya ce shugabannin Larabawa 'yan kasar Amurka sun yi magana da Fadar White House cewa sun damu game da tasiri kan 2024, kuma sun sanarwa da Biden wannan batu.
Wasu karin manyan 'yan Democrat a Michigan sun bayyana irin wannan damuwa.
Aiyash said. Alyash ya ce "Tabbas babu wani daga cikin mu da ke son ganin bala'in shugabancin Trump sau biyu. Amma mu ma ba za mu zauna mu nade hannaye kawai mu bai wa Biden dama ta biyu ba idan ba a biya mana bukatunmu ta hanyar martani na girmamawa ba."
Michigan na da mafi yawan Larabawa 'yan kasar Amurka inda sama da mazaunan jihar 310,000 sun fito ne daga Gabas ta Tsakiya ko Arewacin Afirka.
Da yawa daga cikin jama'ar na alkawarin ba za su sake baiwa Biden kuri'a ba har sai ya yi kira da a tsagaita wuta a yakin.
Musulmai ne suka sanya Biden ya yi nasara a Michigan
Ya nade hannaye ya yi shiru, yana sake goyon bayan 'yancin Isra'ila na kare kanta bayan harin 7 ga Oktoba wanda hakan ke sanya shakku kan hasashen da Ma'aikatar Lafiya ta Gaza ta yi game da adadin Falasdinawan da suka mutu.
Wannan mataki ya sauya a ranar Larabawa a lokacin da Biden ya mayar da martani ga zanga-zangar da aka yi don kiran a tsagaita wuta da tare kudade a Minnesota, inda ya ce akwai bukatar a dakata a rikicin Gaza, don samun damar kwashe fursunonin yaki.
"Dakatawa na nufin bayar da lokaci a kwashe fursunonin yaƙi," in ji shi.
Kusan shugabannnin Larabawa 'yan Amurka 30 da kuma masu fafutuka ne suka taru a wajen garin Detroit a ranar 16 ga Oktoba don tattauna martanin gwamnatin Biden ga yakin.
Wani daga cikin wadanda suka halarci taron, Hussein Dabajeh ya fara kafa wani kwamiti na siyasa da zai yi bore ga 'yan takarar Democrats da suka ki magana don kalubalantar Isra'ila saboda hare-haren kan mai uwa da wabi da suke kai wa tare da kashe fararen hula.
Dabajeh da sauran shugabannin jama'a sun ce a yayin da Larabawa - Amurkawa da dama ba za su goyi bayan dan takarar Republican ba kamar irin su Trump, za su iya ƙin ma jefa ƙuri'a gaba daya.
Trump ya yi nasara a Michigan da tazarar ƙuri'a 10,000 a 2016, inda dubban 'yan Michigan suka yanke shawarar ƙin jefa ƙuri'a a zaben.
Al'ummar Musulmai da dama na yankin Wyne sun taimaka wa Biden samun nasara a jihar a zbaen 2020 da tazarar kuri'u kusan 154,000.
Biden ya ji daɗin wannan dama a Dearborn, inda kusan rabin jama'ar garinsu 110,000 Larabawa ne.