Sojojin Nijeriya sun ce sun ci karfin mayakan Boko Haram ko da yake suna ci gaba da kai hare-haren sari-ka-noke./Hoto: Reuters

Mayakan Boko Haram sun sace mata akalla 42 a wani hari da suka kai a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya, kamar yadda mazauna yankin suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press a ranar Laraba.

‘Yan kungiyar sun far wa matan ne a lokacin da suka je yin itace a karamar hukumar Jere, wurin da ya kasance cibiyar yaki da 'yan ta'adda na Boko Haram, da aka kwashe shekara 14 ana ana fafatawa da su, in ji wani mamba na kungiyar sa-kai ta Civilian Joint Task Force, mai suna Abba.

Kazalika mazauna yankin sun ce matan da aka sace sun fito ne daga sansanin ‘yan gudun hijira da ke Mafa wanda ke makwabtaka da su, kuma suna sayar da itace ne domin samun kudin amfanin yau da gobe sakamakon matsin tattalin arziki.

Kachalla Maidugu, mai magana da yawun gwamnati a yankin, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata, amma sai da yammacin Laraba aka fitar da sanarwar.

“Mun samu labarin a jiya cewa an sace mata 46, amma hudu kawai aka bari su koma gida yayin da sauran mata 42 aka tafi da su,” in ji Maidugu.

Ya ce mayakan sun bukaci a biya naira 50,000 don fansa kan kowace mace.

An sace matan ne sa’o’i kadan bayan mayakan Boko Haram suka yi wa jami’an tsaro da ke kare manoma a yankin kwanton-bauna, a cewar Abba da kuma kungiyar tsaro ta yankin.

Akalla mutane 35,000 ne aka kashe tare da raba mutane miliyan 2.1 da muhallansu sakamakon tashe-tashen hankulan Boko Haram, a cewar bayanai daga hukumomin Majalisar Dinkin Duniya a Nijeriya.

AP