A wani matakin kafa tarihi na magani, wasu rukunin likitoci a Oxford sun samu nasarar yin dashen mahaifa a karon farko a Ingila a ranar Larabar nan.
Wannan tiyata na bayar da fata nagari ga mata, wadanda ake haifa da matsalar mahaifar da ba ta aiki, kuma a karshe suke samun damar daukar ciki su haihu.
Wata sanarwa da Asibitin Jami'ar Oxford ta fitar ta ce wadda aka yi wa dashe da wadda ta bayar da kyautar mahaifarta masu shekara 34 na cikin koshin lafiya.
Wadda aka yi wa dashen a yanzu na shirin karbar magani ta hanyar IVF, inda za a yi amfani da kwayoyin haihuwa na mijinta da nata don ta samu ciki.
Kwararrun likitocin da suka yi wannan aiki sun samu jagorancin kwararru da Asusun Kiwon Lafiya na Kwalejin Lafiya ta Imperal da Jami'ar Oxford.
Mahaifar da aka sadaukar
Farfesa Richard Smith, shugaba kuma wanda ya kafa kungiyar 'Charity Womb Transplant UK' ya bayyana cewa "Wannan ne karo na farko a Ingila bayan bincike na shekara 25, kuma an samu nasararsa, godiya ga 'yar'uwar mara lafiyar da ta yarda ta sadaukar da mahaifarta."
"Har yanzu lokacin ya yi wuri, amma kuma idan komai ya ci gaba da tafiya yadda ya kamata, wadda aka yi wa dashen za ta samu ci gaba, za kuma ta kai matakin wadda za ta iya daukar ciki, ta haihu a shekaru masu zuwa.
Muna godiya ga Asusun Dashen Mahaifa na Ingila da ya dauki nauyin aikin, da kuma kwararrun likitocinmu da suka nuna kwarewa da sadaukar da lokutansu."
"Duk wani dashe da za a yi a nan gaba, zai ta'allaka ne ga amincewar wanda zai sadaukar da mahaifa, da kuma kudaden da za a yi aikin da su, wadanda ake samu ta hannun Asusun Dashen Mahaifa na Ingila.
"Amma kuma, muna fatan a nan kusa za mu taimaka wa mata su haihu ba tare da mahaifa ba ko kuma tare da mahaifar da ba ta aiki sosai."
A Ingila, daya daga cikin mata 5,000 na zuwa duniya ba tare da lafiyayyar mahaifa ba, wanda hakan ke hana su daukar ciki.
Haka zalika, mata da yawa na fuskantar matsalar cire musu mahaifa sakamakon cututtuka da yawa, da suka hada da ciwon daji.
A yayin da wannan ne karo na farko da Ingila ta yi dashen mahaifa, a duniya an yi wannan aiki kusan sau 100, wanda ya bayar da damar haihuwar jarirai 50.