Ana yawan samun kisa ta hanyar amfani da bindiga a Amurka. Hoto/AA

Wani mutum farar fata dauke da wata bindiga mai karfi da karamar bindiga ya kashe bakar-fata uku a kantin Dollar General da ke birnin Jacksonville na Jihar Florida.

Lamarin ya faru ne a ranar Asabar inda jami’an tsaro a birnin ke ganin lamarin bai rasa nasaba da kiyayya ga bakar-fata.

Rahotanni sun tabbatar da cewa mutumin ya kashe kansa bayan ya kashe mutanen uku.

“Nuna wariyar launin fata ne ya tunzura wannan harbin, kuma ya tsani bakaken mutane,” kamar yadda jami’in dan sanda na birnin Jacksonville, T.K Waters ya shaida a wani taron manema labarai.

Mutumin da ake zargin wanda Mista Waters ya kira da farar fata namiji ne, ba a bayyana ko wanene ba.

Mista Waters ya ce duka wadanda aka kashe bakaken fata ne, maza biyu da mace daya.

Mista Waters ya kara da cewa ana ganin wanda ya yi harbin ya yi gaban kansa ne ba tare da agajin wani ba, kuma kafin ya aikata wannan danyen aikin, ya yi rubuce-rubuce da dama ga kafafen watsa labarai da iyayensa da kuma hukumomi kan yadda ya tsani bakar fata.

‘Yan sandan birnin dai sun ce tuni suka kaddamar da bincke kan wannan lamarin.

Ana yawan samun kisan mutane ta hanyar amfani da bindiga a Amurka.

Ko a watan Mayun da ya gabata sai da wani dan bindiga ya kashe mutum takwas a arewacin birnin Dallas da ke Jihar Texas ta Amurka.

Reuters