Cibiyar tattara bayanai kan kyamar Musulunci da nuna ƙiyayya ga Musulmai ta yi ƙira kan a ƙara mai da hankali bisa ƙaruwar rahotanni da ake samu na nuna kyama ga Musulumai da addininsu. /Hoto: Taskar Labarai na Reuters      

Ƙasar Austria ta samu adadi mafi yawa na rahotannin nuna ƙyamar addinin Musulunci a bara tun bayan da ta soma tattara bayanai kan lamarin a shekarar 2015, a cewar wani rahoto.

Hakan ya fito ne cikin rahoton shekara-shekara da Cibiyar Tattara Bayanai kan ƙiyayya da nuna ƙyama ga addinin Musulunci da kuma wariya ga Musulmai ''Documentation Centre on Islamophobia and Anti-Muslim Racism'' ta fitar a ranar Litinin a shafinta na intanet.

Adadin rahotannin da aka tattaro sun nuna yadda lamarin ya yi ƙamari sosai tun bayan barkewar yakin Isra'ila a Gaza a ranar 7 ga watan Oktoba shekarar da ta gabata, in ji rahoton.

An samu ƙarin rahotanni kan lamarin tun daga watan Oktoba zuwa Disamba fiye da watanni taran farkon na shekarar 2023.

Makarantu su ne wauraren farko da aka fi samun rahotanni ƙararrakin tun daga watan Oktoba, in ji rahoton.

A bangaren ilimi, iyaye da dalibai har ma malamai sun shigar da ƙarar nuna ƙiyayya da ƙyama ga addinin Musulunci.

Baki ɗaya dai, kashi 66.7 cikin 100 na yawan rahotannin da aka tattaro sun faru ta kafofin intanet,kashi 33.7 cikin 100 kuma ba ta intanet ba.

Kazalika kusan kashi 87.8 cikin 100 na rahotannin da aka tattaro daga kafofin intanet sun shafi kamalan nuna ƙiyayya.

An wulakanta Musulmai kana ana kwatanta su da dabbobi a cikin muhawara da dama da ake yi a shafukan intanet, a cewar rahoton.

Da yawa daga cikin zantukan kuma kan danganta alhakin ƙyamar Yahudawa a kan Musulmai, in ji rahoton.

Haka kuma kashi 40 cikin 100 na duka rahotannin da aka tattaro sun bayyana rashin samun daidaito sannan kashi 19.5 cikin 100 suka yi nuni da keta mutunci.

Adadin yaduwar ƙiyayya ya kai kashi 8.9 cikin 100 yayin kashi 2.6 cikin 100 suka yi nuni da cin zarafi ta hanyar kai hari ga jiki.

A cikin rahotonta, cibiyar tattara bayanan ta jaddada cewa alkalumanta da ta tattaro a rubuce suke amma akwai yiwuwar ainihin adadin rahotannin ƙiyayya da nuna wariya ga addini Musulunci sun yi matukar zarce yanda ake tsammani.

Cibiyar ta bayyana alkaluman da ta tattaro a matsayin "mataki da ke da matukar damuwa" yanayin da ke ci gaba da samar da rarrabuwar kawuna a cikin al'umma.

Don haka ta yi kira kan a ɗaɗa mai da hankali kan batun ƙiyayya da nuna kyamar ga Musulunci.

AA