Babban mai ba da shawara kan harkokin tsaro a Amurka Jake Sullivan ya gana da Yariman Saudiyya mai jiran gado Mohammed bin Salman a wata ziyara da ya kai kasar, inda suka yi nazari kan abin da Fadar White House ta kira da "gagarumin ci gaba" a kokarin samar da zaman lafiya a kasar Yemen.
A wata ziyarar da ya kai a ranar Lahadin da ta gabata da nufin karfafa dangantakar da ke tsakanin Amurka da Riyadh, Sullivan ya zanta da Yariman da Sheikh Tahnoon bin Zayed al Nahyan, mai ba da shawara kan harkokin tsaron kasa na UAE da takwaransa na Indiya Ajit Doval.
"Sun yi tattaunawar ne don bayyana mahangarsu ta hadin gwiwa ga ci gaban yankin Gabas ta Tsakiya da ke da alaka da Indiya da sauran kasashen duniya, "in ji Fadar White House.
Ganawar ta Sullivan ya biyo bayan tsamin dangantaka da aka samu tsakanin Amurka da Saudiyya sakamakon matakin rage hako mai da Saudiyya wacce ke jagorantar kungiyar OPEC ta dauka.
"Ya yi nazari sosai kan ci gaban da aka samu a tattaunawar da ake yi na kara tabbatar da tsagaita bude wuta da aka kwashe tsawon wata 15 ana yi a Yemen, ya kuma yi maraba da kokarin MDD na kawo karshen yakin, da kuma batutuwa da dama," a cewar sanarwar da fadar White House ta fitar.
Kokarin samar da sulhu na dindindin
Sanarwar ta kara da cewa, Sullivan ya kuma mika godiyar Amurka ga Yarima Salman mai jiran gado bisa goyon bayan da Saudiyya ta bai wa 'yan Amurka a lokacin da aka kwashe su daga Sudan.
Wakilin Amurka na musamman Tim Lenderking ya je kasashen Oman da Saudiyya a farkon wannan watan domin neman hanyoyin da za a samar da zaman lafiya a Yemen, in ji Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka.
A shekarar 2015 ne sojin kawance da Saudiyya ke jagoranta suka shiga kasar Yeman bayan da Iran da ke da alaka da Houthi suka fatattaki gwamnati daga Sana'a, babban birnin kasar.
Tawagar Saudiyya da ke neman cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta dindindin don kawo karshen sanya hannun dakarun soji a yakin, ta kammala tattaunawar sulhu a tsakiyar watan Afrilu a birnin Sanaa da kungiyar Houthi, wadda babban mai shiga tsakani ya ce an samu ci gaba, kuma za a ci gaba da tattaunawa.
Wani babban jami'in tsaron Isra'ila ya fada a ranar Juma'a cewa Isra'ila na fatan samun nasara a kokarin daidaita alakarta da Saudiyya a ziyarar da Sullivan ya kai can.
Sai dai sanarwar da fadar White House ta fitar ba ta ambaci Isra'ila ba.