Wasu Yahudawa ‘yan kama-wuri-zauna sun ƙona wani masallaci a arewa maso yammacin birnin Jericho da ke Gaɓar Yammacin Kogin Jordan a ranar Lahadi, kamar yadda wani ɗan gwagwarmaya a yankin ya tabbatar.
Hasan Mleihat na kungiyar kare hakkin Larabawa makiyaya ya shaoda cewa Yahudawan sun kuma ƙona wata tarakata a cikin al’ummar Mleihat Bedouin.
“Sun ƙona masallacin baki ɗaya, sai dai mazauna yankin sun yi ƙoƙarin kashe wutar da ta kama a tarakatar,” kamar yadda ya ƙara da cewa.
Yahudawa ‘yan kama-wuri-zauna sun kai hare-hare fiye da 2,970 a shekarar 2024 a kan Falasɗinawa da dukiyoyinsu a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye, kamar yadda alƙaluman Falasɗinu suka nuna.
Aƙalla Falasɗinawa 10 aka kashe tare da lalata bishiyoyin zaitun 14,000 a yayin harin.
Kimanin Yahudawa ‘yan kama-wuri-zauna 770,000 ne ke zaune a wurare 180 da suka mamaye a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan.