Momika, dan asalin kasar Iraki da ke zaune a Sweden ya kona Kur'ani karkashin kariya da 'yan sanda suka ba shi a gaban Babban Masallacin Stockholm ranar Sallar Layya. / Photo: Reuters Archive

Wani Kirista dan kasar Iraki ya ki sayar wa mutumin da ya kona Kur'ani a Sweden lemon kwalba daga shagonsa, saboda jin takaicin abin da ya yi na wulakanta Musulunci.

Ibrahim Sirimci, wanda ke da kantin sayar da abinci a babban birnin Sweden Stockholm, ya yi kememe ya ki sayar wa Salman Momika lemon kwalbar.

Mai kantin sayar da abincin ya nadi bidiyon abin da ya farun tare da yadawa a shafukan sada zumunta.

Kazalika wani Kiristan dan kasar Iraki da shi ma yake cikin kantin a lokacin, ya shaida wa Momika cewa "Ni ma dan Iraki ne, ni Kirista ne. Abin da ka yi abin kunya ne da tur. Ka ci mutuncin Musulunci. Ka bata mana rai kamar yadda ka bata wa mutane da dama."

Yayin da yake magana da kamfanin dillancin labarai na Anadolu, Sirimci ya ce Momika ya je kantinsa ne sayen lemon kwalba kuma da ya gane shi sai ya ce ba zai sayar masa ba.

Sirimci ya ce: "Ya zo kantina don ya sayi lemon kwalba. Na gane shi sai na ce masa, 'Kai ne wanda ka kona Kur'ani, don haka ba zan sayar maka da lemo ba."'

Momika, dan asalin kasar Iraki da ke zaune a Sweden ya kona Kur'ani karkashin kariya da 'yan sanda suka ba shi a gaban Babban Masallacin Stockholm ranar Sallar Layya.

A ranar 20 ga watan Yuli ne Momika ya sake yaga Kur'ani tare da tutar kasar Iraki a yayin da 'yan sanda suke ba shi kariya a gaban Ofishin Jakadancin Iraki da ke birnin Stockholm.

AA