Fafaroma Francis ya bayyana 'yan takarar biyu a matsayin "mugwayen mutane" amma ya ƙara da cewa "dole ne ku zabi mai ɗan dama-damar". /Hoto: TRT World

Fafaroma Francis ya buƙaci mabiya ɗarikar Katolika na Amurka da su “zaɓi mai ɗan dama-dama a cikin mugwaye biyu" tsakanin 'yar takarar Jam’iyyar Democrat kuma Mataimakiyar Shugaban Ƙasa Kamala Harris da abokin hamayyarta na Jam’iyyar Republican, tsohon shugaban ƙasa Donald Trump.

Gabanin zaben da aka shirya yi a ranar 5 ga watan Nuwamba, Fafaroma Francis ya bayyana 'yan takarar biyu a matsayin "mugwayen mutane" amma ya ƙara da cewa "dole ne ku zabi mai ɗan dama-damar".

“Wane ne mai ɗan dama-damar a mugunta? Waccan matar, ko wancan mutumin? Ban sani ba. Kowane mutum na da hankalinsa, dole ne ya yi tunani kuma ya yanke wannan shawarar, ”in ji Fafaroma mai shekaru 87, ba tare da kama sunan wanda yake nufi ba tsakanin Harris da Trump, a ƙarshen ziyarar da ya yi a yankin Asiya.

"Dukkan biyun suna adawa da rayuwa," in ji shi, yana mai nuni da rashin amincewarsa kan manufofin da yake ganin suna cutar da mutuncin ɗan'adam, ko da ya shafi manufar baƙin haure ko ta zubar da ciki.

A matsayinsa na shugaban Cocin Katolika kuma mai mulkin birnin Vatican, Fafaroma Francis yana da gagarumin tasiri a tsakanin mabiya ɗarikar Katolika mai kimanin mutum biliyan 1.4 a faɗin duniya.

Doka ta hana Fadar Vatican yin katsalandan a cikin harkokin siyasa ko zaɓukan ƙasashe.

Duk da haka, a cewar John L. Allen, wani masani kan harkokin Fadar Vatican kuma editan Crux - wanda ya ƙware a watsa labarai da ra'ayoyi kan Vatican da Cocin Katolika - Fafaroma Francis ya shiga tsakani a wasu lokuta, "daga batun ƙaura zuwa muhalli da kuma zubar da ciki zuwa batun jinsi.

"Abin da ba a saba gani ba shi ne cewa ba ya magana kan takamaiman zaɓuka ko 'yan takara, amma duk da haka, ba wai ba ya yi ba ne gaba ɗaya," Allen ya shaida wa TRT World.

Sai dai, a cewar Allen, tsoma bakin Fafaroma "ya kan jawo kanun labarai amma ba ya sauya ƙuri'a da gaske" kuma maiyuwa ba zai yi tasiri ga yanke shawarar al'ummar Katolika miliyan 52 na Amurka ba.

“Gaba ɗaya, ’yan Katolika na Amirka suna yin zaɓe ne bisa ga abubuwan da suke so na siyasa maimakon duk abin da Fafaroma ko bishop-bishop za su ce,” in ji mai sharhin.

A kan Isra'ila, zubar da ciki da ƙaura

A game da yakin Gaza - ana saura makwanni kadan ya cika shekara guda - Fafaroma ya bayyana rashin jin dadinsa game da rashin samun ci gaba wajen cimma yarjejeniyar zaman lafiya don kawo karshen ta'asar Isra'ila da ta kashe Falasdinawa sama da 41,000.

"Ku gafarce ni da faɗar haka, amma ban ga wani ci gaba da aka samu wajen samar da zaman lafiya ba," kamar yadda ya shaida wa manema labarai a cikin jirginsa, inda ya kira harin da Isra'ila ta kai a kwanan baya a makarantar da ta kashe yara da "mummuna".

Kalaman Fafaroman sun fi mayar da hankali kan manufofin tsohon shugaban kasar Donald Trump na shige da fice, wadanda suka hada da shirin korar miliyoyin baƙin haure, da kuma goyon bayan da Mataimakiyar Shugaban Ƙasa Kamala Harris ke yi kan hakkin zubar da ciki.

Fafaroman ya ce rashin maraba da baƙin haure babban zunubi ne sannan ya kwatanta zubar da ciki da "kisan kai".

Reverend Robert Gahl, mataimakin farfesa a Makarantar Kasuwanci ta Busch a Jami'ar Katolika ta Amurka, ya bayyana wa TRT World abin da Fafaroma yake nufi da "mai ɗan dama-dama a mugwayen biyu".

"Zai zama kuskure a yi tunanin cewa kalamansa na "mai ɗan dama-dama a cikin mugwayen biyu" tana nufin irin ɓarnar da wani aiki ko manufa za su iya haifarwa kawai," in ji shi.

A nasa bangaren, Reverand Gahl yana ganin yana da muhimmanci a bambance tsakanin ka'idodin dabi'u na asali da kuma hukunce-hukuncen hankali.

‘Rashin yin zaɓe yana da muni'

Fafaroma Francis ya kuma bukaci kowane dan darikar Katolika da ya kada kuri'a, yana mai cewa "rashin kada kuri'a abu ne marar kyau".

Reverend Gahl ya yi cikakken bayani game da muhimmancin ƙuri'ar Katolika a zaben Amurka.

"Al'ummar Katolika a Amurka muhimmin ɓangare ne ga jefa kuri'a a duk zabe takara," in ji shi. Katolika suna wakiltar wani yanki mai mahimmanci na masu zaɓe, tare da fiye da kashi 20 na manya a cikin manyan jihohin yaƙi irin su Pennsylvania da Wisconsin da aka bayyana a matsayin Katolika.

Ko yaya dai, Katolika yawanci ba sa jefa kuri'a iri daya saka a matsayin mabiya ɗariƙa ɗaya.

Bayanai na tarihi daga Cibiyar Bincike ta Pew sun nuna cewa ’yan Katolika na Amurka sun “rarrabu sosai a ra'ayoyi” a cikin dangantakarsu ta siyasa.

Cibiyar ta ce kusan kashi 52 na darikar Katolika na Amurka suna goyon bayan jam'iyyar Republican, yayin da kashi 44 cikin 100 ke karkata zuwa jam'iyyar Democrat.

Ga Allen, "Yaƙin koyaushe yana kan wannan kashi 10 ko makamancin haka a tsakiya".

'Yar takara ta uku a takarar shugaban kasa, Dr Jill Stein ta Jam'iyyar Green Party, duk da haka, ba ta amince da ra'ayin Fafaroma kan Trump da Harris ba.

“Babu wani ɗan dama-dama a cikin mugwayen. Duk manyan mugwaye muke da su guda biyu, ”in ji Stein a wani sakon da ta wallafa a shafin sada zumunta.

Stein ta fito fili tana sukar ayyukan Isra'ila a Gaza kuma tana adawa da korar baƙin haure. Ta kuma ayyana samun damar zubar da ciki cikin aminci a matsayin "hakkin dan'adam da ba za a ɗauke ido a kansa ba".

TRT World