Labanon

1614 GMT — Isra'ila ce za ta dauki alhakin kai hare-haren Lebanon — Hamas

Babban jami'in kungiyar Hamas Izzat al-Rasheq ya ce gwamnatin Isra'ila ce za ta dauki nauyin sakamakon "wannan ci gaba da kai hare-hare kan kasar Lebanon" bayan fashwar na'urorin sadarwa na kungiyar Hizbullah a kudancin Lebanon da kuma yankunan Beirut.

1031 GMT — Ministan Lafiya na Lebanon Firass Abiad ya bayyana cewa mutum 12 suka rasu bayan wasu na'urori na sadarwa waɗanda mambobin Hezbollah ke amfani da su sun yi bindiga a lokaci ɗaya a ranar Talata.

"Bayan duba duka asibitoci", an sake sabunta adadi waɗanda suka rasu zuwa "12 ciki har da yara biyu da suka jikkata", kamar yadda Abiad ya shaida wa taron manema labarai, inda ya saka adadin waɗanda suka jikkata tsakanin 2,750 da 2,800.

Wasu daga cikin waɗanda suka jikkata a Bekaa da ke gabashin Lebanon "an kai su Syria", inda "wasu daga cikinsu an kai su Iran", in ji shi.

TRT Afrika da abokan hulda