Kashi 53 cikin 100 na mutanen Faransa suna son gwamnatin Firaministan Faransa Michel Barnier ta faɗi domin fushi kan ƙudurin kasafin kuɗinsa, in ji wata ƙuri’ar jin ra’ayin jama’a da kamfanin Ifop-Fiducial ya gabatar wa gidan rediyon Sud Radio.
Ƙuri’ar jin ra’ayin jama’ar ta nuna cewa kashi 67 cikin 100 na jama'ar ƙasar sun ƙi amincewa da kasafin kuɗin Barnier, wanda ke neman rage giɓin kasafin kuɗin Faransa da ke hauhawa ta hanyar ƙara haraji da ya kai dala biliyan 63 tare da rage kuɗin kashewa, yayin da kashi 33 cikin 100 na mutanen suka goyi bayan kasafin kuɗin.
Gwamnatin Barnier za ta iya faɗuwa kafin Kirsimeti, ko kuma ta iya faɗuwa nan da mako mai zuwa, idan ƴan adawa masu tsattsauran ra’ayin ƴan mazan jiya da masu sassaucin ra’ayi suka samu suka tilasta gatabar da ƙudurin ƙin amincewa inda zai iya faɗi, in ji gwamman majiyoyi a fagen siyasar ƙasar.
Ƙuri’ar jin ra’ayin da kamfanin Ifop-Fiducial ya gabatar ya dogara ne kan yi wa mutane 1,006 tambayoyi tsakanin ranar 26 da ranar 27 ga watan Nuwamba.
A wata ƙuri’ar jina ra’ayin jama’a da aka yi a madadin gidan talabijin ɗin BFM TV ranar Laraba, kashi 63 cikin 100 na waɗanda aka yi wa tambayoyi sun ce ya kamata Shugaba Emmanuel Macron ya yi murabus idan gwamantin Barnier ta fadi.