Turkiyya za ta ɗauki tsauraran matakai kan Isra'ila wadda take ƙoƙari ta hana Ankara bayar da tallafi ga Falasɗinawa, in ji Daraktan Sadarwa na ƙasar Fahrettin Altun.
“Abubuwa da dama da sashenmu na watsa labarai da sauran sassa suke yi a ciki da wajen ƙasa suna tare da wannan matsaya,” kamar yadda Altun ya bayyana a shafin X a ranar Litinin.
Turkiyya na daga cikin ƙasashen da suka fi mayar da hankali wurin kai kayan agajin jin ƙai Falasdinu.
"Tun ranar 7 ga watan Oktoba, Turkiyya ta bankaɗo ƙarairayin Isra'ila da dama, da kuma yadda wasu kafafen watsa labarai na duniya suka faɗa tarkonta na labaran ƙarya," in ji Altun.
Ya ce ƙasarsu ta daɗe tana kira a yi adalci da kuma biyan buƙatun Falasɗinawa, musamman daga shekaru 20 da suka gabata da kuma lokacin da aka soma kai hare-hare na ranar 7 ga watan Oktoba.
"Turkiyya ta amince da kasancewar yankin Falasɗinu a matsayin ƙasa mai ƴancin kanta da ke da babban birninta a Gabashin Birnin Ƙudus kamar yadda iyakokin shekarar 1967 suka tanadar," in ji Altun.
Yaƙin da labaran ƙarya
Da yake tsokaci kan illolin labaran ƙarya, Altun ya ce suna jawo rashin jituwa da cutarwa a cikin al'umma, yana mai bayyana cewa magance wannan matsala a ƙasar da ma ƙasashen duniya yana da matuƙar muhimmanci.
Ya jaddada muhimmancin kare mutuncin Falasɗinawa, yana mai cewa hakan tamkar kare mutuncin ɗan'adam ne.
Altun ya ce a baya-bayan nan Turkiyya ta yi fama da masu watsa labaran ƙarya, musamman game da cinikayya, waɗanda suke cewa Ankara ba ta goyon bayan Falasɗinu.
"Muna so mu jaddada wa masu sukar Turkiyya da gangan da kuma waɗanda ba su sani ba cewa matsayinta na goyon bayan Falasɗinu tun daga 7 ga watan Oktoba ba zai sauya ba kuma ba za ta daina sukar Isra'ila kan kisan kiyashin da take yi ba."