Daraktan Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun ya yi tir da harin da Isra'ila ta kai wa ƴan jarida a sansanin ƴan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiya Gaza, wwanda ya jikkata ƴan jarida da dama ciki har da na TRT Arabi .
"Duk abin da zai faru sai dai ya faru, amma ba za mu daina gaya wa duniya gaskiya game da muguntar da Isra'ila take yi wa fararen-hula a Gaza ba," in ji Altuna hira da TRT bayan harin da Isra'ila ta kai ranar Juma'a.
Ya ce Tel Aviv yana yaƙi da masu faɗar gaskiya shi ya sa take kai hari da "gangan" kan ƴan jarida.
"Isra'ila ta kwashe tsawon lokaci tana tafka ɓarna. Tana yin haka ne saboda ƙasashen Yamma ba sa adawa da matakin da take ɗauka," in ji Altun.
Mai ɗaukar bidiyo da hotuna na TRT Sami Shehadeh, wanda ke daga cikin tawagar ƴan jaridar da ke aiko da labarai daga sansanin ƴan gudun hijirar da ke tsakiyar Gaza, ya samu mummunan raunuka har ma aka yanke ƙafarsa sakamakon harin da tankar yaƙin Isra'ila ta kai musu ranar Juma'a
Wakilin TRT Arabi Sami Berhum da wasu ƴan jarida su ma sun jikkata. Ganau sun ce da gangan Isra'ila ta kai hari kan ƴan jaridar.
Darakta Janar na TRT Zahid Sobaci ya yi Allah wadarai da harin, yana mai bayyana Isra'ila a matsayin "maƙetaciya, maras mutunci da ba ta kiyaye doka da yanayi na jinƙai."
Mataimakin Shugaban Jam'iyyar AK kuma mai magana da yawunta Omer Celik ya yi tir da harin sannan ya jajanta wa ƴan jaridar da lamarin ya shafa.
"Muna sake yin Allah wadarai da sojojin Isra'ila, waɗanda suka kashe Falasɗinawan Gaza, tare da ƴan jarida da ke aiki agajin jinƙai," kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X.
Ba wannan ne karo na farko da sojojin Isra'ila suka kai hari kan ƴan jarida ba a Gaza a yayin hare-haren da suka kwashe watanni shida suna kai wa yankin ba. A cewar Ofishin Watsa labara na Gaza, Isra'ila ta kashe ƴan jarida aƙalla 140 tun da ta ƙaddamar da hare-hare a Gaza.