Yawan waɗanda suka rasa rayukansu sakamakon tsananin zafi rana a Hajjin bana ya kai 922, inda 600 daga cikinsu suka kasance 'yan ƙasar Masar ne. / Hoto: AFP

Adadin wadanda suka mutu a aikin Hajji na bana da aka yi a kasar Saudiyya sakamakon yanayin tsananin zafi ya haura 900.

Wani jami'in diflomasiyyar Larabawa ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP a ranar Laraba cewa mutanen da suka mutu a cikin alhazan Masar kadai sun haura zuwa "aƙalla 600" daga sama da 300 a rana daya da ta gabata, galibi saboda tsananin zafin ranar da da wahala a jure masa.

Adadin ya sa jumullar waɗanda suka mutu zuwa yanzu ya kai 922, kamar yadda alƙaluman da AFP ya tattara waɗanda ƙasashe da dama suka fitar suna nuna.

Daga baya jami'in diflomasiyyar ya ƙara da cewa jami'an Masar a Saudiyya sun kuma samu rahoton ɓatan alhazai," ciki har da 600 da suka rasa rayukan nasu.

Mabrouka bint Salem Shushana 'yar ƙasar Tunisiya, wadda ke cikin shekarunta na 70 ta ɓata tun a ranar hawan Arafa, kamar yadda mijinta Mohammed ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP a ranar Laraba.

Ya ce ba ta samu damar shiga wajen da aka tanada mai na'urar sanyaya waje ba saboda ba a mata rajista ba kuma ba ta da izinin yin Hajji.

"Ta tsufa. Ga shi kuma tagaji. Tana jin zafi sosai kuma babu wajen da za ta iya bacci," ya faɗa.

"Na duba ta a duka asibitocin, Amma har yanzu babu alamarta."

An yi ta watsa cigiyar hotunan waɗanda ba a gani ba a Facebook da sauran shafukan sada zumunta don samun bayanai.

Cikin masu neman bayanai har da 'yan'uwa da ƙawayen Ghada Mahmoud Ahmed Dawood, wata 'yar ƙasar Masar da ba a gan ta ba tun ranar Asabar.

"'Yarta ta min waya daga Masar tana roƙona da na wallafa saƙo a Facebook wanda zai iya taimakawa a gano ta," in ji wata 'yar'uwarsu da take zama zama a Saudiyya.

"Abin daɗin dai shi ne har yanzu ba mu ga sunanta a jerin mutanen da suka mutu ba, wanda hakan ya sa muke fatan cewa tana raye."

Houria Ahmad Abdallah Sharif mai shekara 70 'yar Masar ma ta ɓata tun ranar Asabar.

Bayan da ta kammala addu'a a kan Dutsen Arafa sai ta gaya wa ƙawarta cewa za ta je banɗaki don wanke abayarta, dawowar da ba ta yi ba kenan.

Tsananin zafi

Aikin Hajji daya ne daga cikin rukunan Musulunci guda biyar kuma duk Musulmin da yake da hali dole ne ya yi shi akalla sau daya. An ƙayyade lokacinsa bisa kalandar watan Musulunci, inda yake sassauyawa a kowace shekara a kalandar Miladiyya.

A cikin shekaru da dama da suka gabata, Hajjin kan faɗo a daidai lokacin bazara a Saudiyya.

Wani bincike na Saudiyya da aka wallafa a watan da ya gabata ya nuna cewa zafi na ƙaruwa da digiri 0.4 a ma'aunin salshiyas a kowace shekara 10.

Baya ga Masar, ƙasashen Jordan da Indonesiya da Iran da Senegal da Tunisiya da Iraƙi ma sun tabbatar da mutuwar mutanensu, ko da yake a lokuta da yawa hukumomi ba su bayyana musabbabin faruwar lamarin ba.

Wani jami'in diflomasiyyar Larabawa na biyu ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP a ranar Laraba cewa jami'an kasar Jordan na neman mahajjata 20 da suka ɓata, ko da yake wasu 80 da aka ce sun ɓace tun farko suna kwance a asibitoci.

Shi ma wani jami'in diflomasiyyar Asiya ya shaida wa kamfanin dilancin labaran AFP cewa akwai "kusan mutum 68 da suka mutu" daga Indiya kuma wasu sun ɓata.

"Wasu (sun mutu) ba tare da wata lalura ba, sannan muna da mahajjata da yawa da suka tsufa. Wasu kuma saboda yanayin tsananin zafi; abin da muke zato kenan," in ji shi.

A bara ma fiye da alhazai 200 ne aka ba da rahoton mutuwarsu, mafi yawansu daga Indonesiya.

TRT World