Tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce zai mika kansa ga mahukunta a Georgia domin fuskantar shari'ar tuhumar da ake yi masa kan zargin yunkurin murde zaben shekarar 2020 a jihar.
"Wani abin mamaki, zan tafi Atlanta, Georgia, ranar Alhamis don mika kaina ga mahukunta, ” kamar yadda Trump ya rubuta a shafinsa na sada zumunta ranar Litinin da daddare, sa’o’i kadan bayan bayyana kudin da zai biya na belin kansa kan dala 200,000.
Wannan dai ya kasance karo na hudu da ake tuhumar Trump tun watan Afrilu, sannan hakan ya sa shi zama tsohon shugaban kasa na farko a tarihin Amurka da ya fuskanci tuhume-tuhume.
Tun daga lokacin, Trump, wanda ke kan gaba a masu neman tsayawa takara a karkashin jam'iyyar Republican, ke fama da shari'o'i.
Fitowar da ya yi a New York da Florida da kuma Washington DC, ta yi matukar jan hankalin kafafen yada labarai , inda jirage masu saukar ungulu ke bibiyar duk wani motsi da ya yi.
Trump ya yi sanarwar ce bayan ya gana da lauyoyinsa da masu gabatar da kara a Atlanta don tattauna cikakkun bayanai game da sharuddan ba da belinsa.
An hana tsohon shugaban amfani da duk wata hanya wajen cin zarafi ko tsorata sauran wadanda ake tuhuma da shaidu da kuma sauran wadanda lamarin ya shafa - ciki har da amfani da shafukan sada zumunta – hakan na cikin takardar sharuddan yarjejeniyar ba da belin da mai shari’a ta gundumar Fulton, Fani Willis da lauyoyin da ke kare Trump suka sanya wa hannu.
Cikin har da wallafa "sakonni a shafukan sada zumunta na intanet ko kuma sake yada abun da wani ko wasu su ka wallafa.
Donald Trump dai ya sha sukar alkaliya Willis tun ma kafin a gurfanar da shi a gaban kotu, kazalika da ya ambaci gwamnan Georgia Brian Kemp, dan jam’iyyar Republican, wanda ya yi watsi da yunkurinsa na murde zaben, a wani sako da ya wallafa a shafukan sada zumunta da safiyar Litinin.
Kazalika yarjejeniyar ta haramta wa tsohon shugaban kasar yin “barazana kai-tsaye ko a kaikaice a kowanne irin yanayi” kan shaidu ko wadanda ake kara, da kuma yin magana ta kowace hanya game da su, sai ta hanyar lauyoyi.