Nijeriya na ɗaya daga cikin mambobin ƙungiyar ƙasashen Musulmai kuma an gayyaci Shugaba Tinubu ne saboda wannan matsayi na ƙasarsa./Hoto:Fadar Shugaban Nijeriya

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu zai yi kira a gaggauta tsagaita wuta tare da neman kawo ƙarshen rikicin Isra'ila da Falasɗinu cikin lumana a taron da zai halarta ranar Lahadi a Riyadh, babban birnin Saudiyya.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Bayo Onanuga ya fitar ranar Asabar da maraice ta ce shugaban zai halarci taron ƙasashen Musulmai da ƙasashen Larabawa ne sakamakon gayyatar da Sarki Salman da Yarima mai jiran gadon sarautar Saudiyya Mohammed bin Salman suka yi masa.

Nijeriya na ɗaya daga cikin mambobin ƙungiyar ƙasashen Musulmai kuma an gayyaci Shugaba Tinubu ne saboda wannan matsayi na ƙasarsa.

"Kazalika Nijeriya za ta jaddada yunƙurin samar da ƙasashe biyu masu 'yancin kansu a matsayin hanyar warware rikicin yankin tare da samar da dauwamammen zaman lafiya," in ji Onanuga.

Tinubu zai je Saudiyya ne tare da rakiyar manyan jami'an gwamnatinsa, da suka haɗa da Ministan Harkokin Waje Ambasada Yusuf Tuggar; Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Sha'anin Tsaro, Mallam Nuhu Ribadu; Ministan Watsa Labarai, Alhaji Mohammed Idris; da Darakta Janar na Hukumar Tattara Bayanan Sirri, Ambasada Mohammed Mohammed.

A yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana na 401 a yau— ya kashe Falasɗinawa aƙalla 43,552 tare da jikkata fiye da 102,765, sannan an yi amanna ɓuraguzan gine-gine sun danne fiye da mutum 10,000.

TRT Afrika