Hoton da kamfanin dillancin labarai na Bahrain ya fitar na nuna Sarkin Bahrain Hamad bin Isa al-Khalifa tare da sauran shugabannin Larabawa a Manama a ranar 16 ga Mayu 2024. / Photo: AFP

Kungiyar Hadin Kan Kasashen Larabawa ta yi kira ga dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya su kasance a yankunan Falasdinawa da kuma babban taron zaman lafiya, a yayin zaman da suka yi a Bahrain, amma kuma sun gaza daukar matakan ladabtarwa na tattalin arziki da siyasa kan Isra'ila.

A sanarwar bayan taron da aka fitar a Manama, kasashen 22 sun yi kira da a "samar da kariya ta kasa da kasa da dakarun zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a yankunan Falasdinawa da aka mamaye" har zuwa lokacin da za a warware rikicin ta hanyar samar da kasashe biyu.

Taron ya kuma amince da kiran da sarkin Bahrain mai karbar baƙi Hamad da Shugaban Kasar Falasdinu Mahmud Abbas suka yi na "gudanar da babban taron kasa da kasa karkashin kulawar Majalisar Dinkin Duniya, don warware batun Falasdinu kan doron samar da kasashe biyu."

A nata martanin, Amurka ta ce wanzuwar dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD a yankunan Falasdinawa na iya kawo tarnaƙi ga kokarin Isra'ila na kassara Hamas.

Taron na shugabannin Larabawa a Bahrain bayan sama da watanni bakwai da fara yaƙin Gaza, ya janyo ce-ce-ku-ce a yankin.

Tun bayan harin bakwai ga Oktoba da Hamas ta kai Isra'ila, kasar ta fara kai munanan hare-hare Gaza.

Hamas ta ce ta kai wa maƙiyanta hari ne don mayar da martani ga harin da Isra'ila ta kai wa Masallacin Kudus, ayyukan 'yan kama guri zauna haramatattu a Yammacin Gabar Kogin Jordan, sannan da manufar dawo da batun Falasdinu kan teburi.

Harin na tsawon awanni da sojojin Isra'ila suka kai a ranar ya kashe sama da mutane 1,130, kamar yadda jami'ai da kafafan yada labaran yankin suka fada.

Mayakan Falasdinawa sun kama fursunoni sama da 250 kuma a yanzu 130 suna nan a Gaza, ciki har da wasu 34 da dakarun Isra'ila ke cewa sun mutu, wasun su kuma sun mutu a hare-haren kan mai uwa da wabi da Isra''ila ta kai.

Yakin aikata kisan kiyashi

Tun wannan lokaci zuwa yau, Isra'ila ta kashe sama da Falasdinawa 35,000 - mafi yawan su jarirai, mata da yara kanana - inda ta jikkata sama da 80,000 sannan ta janyo karancin kayan more rayuwa.

Isra'ila ta kassara Gaza ta hanyar rufe hanyoyin shiga yankin, inda ta bar jama''ar yankin musamman na arewacin Gaza cikin yunwa.

A Yammacin Gabar Kogin Jordan da aka mamaye, an kashe kusan Falasdinawa 500 tare da jikkata dubunnai tun 7 ga Oktoba, tare da kame mutane kowace rana.

Kashi 85 na jama'ar Gaza su miliyan 2.4, Falasdinawa sun guje wa gidajensu tun bayan mamayar yankin da Isra'ila ta yi, inda aka raba da yawa daga ciki da matsugunansu.

An zargi Isra'ila da aikata kisan kiyashi a Kotun Kasa da Kasa, wadda ta umarci Tel Aviv da ta tabbatar mayakanta ba su aikata kisan kiyashi ba, sannan su dauki matakan tabbatar da an kai kayan taimakon jinkai ga fararen hula a yankin.

Wannan ne karo na farko da kungiyar ta gudanar da taro tun bayan wanda ta gudanar na gaggawa a Riyad, babban birnin Saudiyya a watan Nuwamba, wanda shi ma ya hada da shugabanni daga kasashe 57 na Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi (OIC), wadda ke da helkwata a birnin Jeddah na Saudiyya.

Ganin yadda ake ta kashe Falasdinawa da kuma yadda Isra'ila ke kin aiki da kiraye-kirayen tsagaita wuta, an yi tunanin ko za a iya samun daukar matakin ladabtarwa ga isra'ila daga taron kasashen Larabawan.

A yayin da a watan Nuwamba shugabanni suka ƙi amincewa da daukar matakin ladabtar da Isra'ila, mai nazari dan kasar Kuwait Zafer al-Ajmi ya fada wa AFP cewa taron na Manama ya sha bamban da taron da aka yi na baya-bayan nan.

Ra'ayin jama'a a Yammacin duniya ya fi karkakata ga nuna goyon baya ga Falasdinawa da magance zaluncin da ake yi musu tun bayan kirkirar Isra'ila shekaru 70 da suka gabata, inji Ajmi.

Hamas ta yi kira ga kasashen Larabawa su "tirsasa" Isra'ila ta kawo karshen hare-haren da suke kai wa Gaza bayan shugabannin kasashen sun gana a Bahrain suna bukatar "Nan da nan a samar da tsagaita wuta mai dore wa".

Saudiyya, daya daga manyan kasashen Kungiyar kuma kasar da ke dauke da waje mafi tsarki a Musulunci, ba ta taba amince wa da Isra'ila a matsayin kasa ba, kuma ba ta shiga Yarjejeniyar Abraham da Amurka ta jagoranci yi a 2020 ba don ganin kasashen yankin Gulf sun sasanta da Isra'ila. Bahrain, Hadaddiyar Daular Larabawa da Morokko sun sasanta da kasar.

'Budadden ciwo'

A ranar Alhamis, kungiyar ta kuma yi kira na daban da a tsagaita wuta a Gaza, sannan a dakatar da raba jama'a da matsugunansu a yankunan Falasdinawa.

Hamas ta yi maraba da sanarwar karshe ta kungiyar inda ta bukaci "'yan'uwa kasashen Larabawa da su dauki matakin da ya dace su tirsasa Isra'ila ta dakatar da mamayar da take yi da kuma kai hare-hare".

Da yake magana a wajen taron. Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya siffanta yakin Gaza a matsayin "budadden ciwo da ke barazanar shafar dukkan yankin", yana mai kira ga "Da a gaggauta sakin fursunoni ba tare da wani sharadi ba".

Guterres ya ce "hanya tabbatacciya guda daya ta kawo karshen rikicin nan ita ce samar da kasashe biyu".

A yayin mayar da martani game da kiran aika dakarun zaman lafiya na MDD, kakakin Majalisar ya ce duk wani yunƙuri na samar da dakaru, ya ta'allaka ne ga "hukuncin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya."

Mataimakain Sakatare Janar na Majalisar ya ce "Abu ne da zai bukaci a tabbatar da shi, kuma ba abu ne da za mu yi wasa da shi ba".

Wannan "Sanarwa ta Manama" da kasashen Larabawa suka sanar ta kuma bukaci "Dukkan bangarorin Falasdinawa da su hada hannu waje guda karkashin Kungiyar 'Yantar da Falasdinawa", wadda gwamnatin Fatah karkashin Abbas ke da mambobi mafi yawa a ciki.

Sanarwar ta kara da cewa suna kallon PLO a matsayin "halastacciyar kungiyar da ke wakiltar Falasdinawa".

Yakin Larabawa da Isra'ila a 1967 ya shaida yadda Isra'ila ta kwace yankunan Falasdinawa a Yammacin Gabar Kogin Jordan, Gabashin Kudus da Gaza.

Daga baya Isra'ila ta mamayi Gabashin Kudus, sannan gwamnatocin Isra'ila da suka biyo baya suka goyi bayan kafa yankunan Yahudawa 'yan kama guri zauna a iyakokin Falasdinawa.

A karkashin dokokin kasa da kasa, yankunan Falasdinawa, da suka hada da Gaza, sun kasance a mamaye, sannan unguwannin Yahudawa na Gabashin Kudus da Yammacin Gabar Kogin Jordan haramtattu ne.

A shekarar 1945 aka kafa Kungiyar Kasashen Larabawa da manufar kare manufofin yankinsu, tare da warware rikici a tsakaninsu.

Sai dai kuma, ana yi wa kungiyar kallon kyanwar lami, kuma ta sha yin gwagwarmayar taimaka wa wajen warware rikice-rikice a Gabas ta Tsakiya, musamman ma mamayar Falasdin mai tarihi da Isra'ila ke yi.

TRT World