Shugabannin ƙasashe sama da ashirin za su haɗu a Rasha mako mai zuwa don taron ƙoli na ƙungiyar BRICS, wadda ƙawance ne na ƙasashe masu tasowa wadda Rasha ke fatan za su ƙalubalanci "danniyar" ƙasashen Yamma.
Taron ƙolin zai zama mafi girma a Rasha tun bayan fara yaƙin Ukraine, kuma yana zuwa ne yayin da shugaban Rasha Vladimir Putin yake son nuna wa Yamma cewa ƙoƙarin yi wa Moscow wariya cikin shekaru biyu da rabin na yaƙin bai yi nasara ba.
Sakataren MDD Antonio Guterres, da Shugaban China Xi Jinping, da shugaban Brazil Luis Inacio Lula da Silva, da shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan suna za su halarci taron a birnin Kazan, daga 22 ga Oktoba zuwa 24.
Rasha ta ce tana sa ran zuwan firaministan India Narendra Modi shi ma.
Moscow ta bayyana ƙoƙarin faɗaɗa BRICS, wanda saunan ya samo asali daga harafin farko na sunayen ƙasashen Brazil, Russia, India, China da Afirka ta Kudu, a matsayin wani ginshiƙin harkokin wajenta.
Babbar ajandar taron ƙoli na ƙungiyar BRICS ya haɗa da tsarin hada-hadar kuɗ tsakanin ƙasashen duniya wanda zai yi gogayya da tsarin SWIFT, sai kuma batun rikicin Gabas ta Tsakiya.
Kremlin ta kira taron a matsayin nasara diflomasiyya wadda za ta taimaka mata wajen gina ƙawance da zai ƙalubalanci "danniyar" Yamma.
Amurka ta yi watsi da batun cewa BRICS za ta zama "abokiyar adawa ta yanki" amma ta bayyana damuwa game da cewa Moscow tana nuna ƙwanjinta a fagen diflomasiyya, yayin da yaƙin Ukraine ke ci gaba.
'Samfurin jagoranci na jama'a'
Gwamnatin Moscow tana ci gaba da nausawa a filin yaƙi a gabashin Ukraine wannan shekara, yayin da take ƙarfafa alaƙa da China, Iran da Koriya ta Kudu, ƙasashe uku da ke abokan faɗan Amurka.
Ta amfani da taruwa BRICS a Kazan, Rasha tana "ƙoƙarin bayyana cewa ba a mayar da Rasha saniyar ware ba, kuma tana da abokai da 'yan uwa," cewar mai sharhi kan siyasa, Konstantin Kalachev wanda ke zaune a Moscow a hirarsu da AFP.
Kotun Duniya ta Manyan Laifuka ICC, ta ayyana shugaba Putin a matsayin wanda ake son kamawa a 2023 kan kwashe yara daga Ukraine, kuma hakan ya sanya shi ƙin halartar taron da aka yi a baya, a Afirka ta Kudu, wadda mamba ce ta ICC.
A wannan karon Kremlin tana son nuna "ita wani tsaɓi ce baya ga Yamma kuma cewa duniya ta koma tsarin ƙasashe da dama," in ji Kalachev, yana nuni da yunƙurin Moscow na matsar da ƙarfin duniya daga Yamma zuwa wasu yankunan.
Shugaba Putin yana yawan maimaita zargin Yamma da "tunzura" Rasha kan aika sojoji Ukraine, kuma ya yi watsi da cewa yaƙin na mamaya ne donƙwace ƙasa.
Kremlin ta ce tana son ya zama al'amuran duniay suna tafiya kan dokar ƙasa-da-ƙasa, "amma ba dokokin da ɗaiɗaikunƙasashe suka kafa ba, wato Amurak."
"Mun yi imani cewa BRICS wani samfuri ne na tsarin ƙasashe da dama, kuma tsari ne da zai haɗa kan Kudanci da Gabashin duniya kan turbar 'yancin ƙasa da girmama juna" in jin hadimi a Kremlin, Yuri Ushakov.
Ya ƙara da cewa, "Abin da BRICS take yi a hankali yake tafiya, daki-daki, ana gida mahaɗa da za ta samar da tsrin duniya mafi daidaiton dimukuraɗiyya".
Yammacin duniya suna kallon Rasha tana amfani da ƙungiyar don faɗaɗa ƙarfin ikonta da ɗaukaka salon labaranta game da rikicin Ukraine.
Ƙungiyar da ta fara da mambobi huɗu sanda aka kafa ta a 2009, a yanzu BRICS ta faɗaɗa zuwa ƙasashe masu tasowa kamar Afirka ta Kudu, Masar, da Iran.
A cewar Ushakov, duka shuwagabannin ƙasashen BRICS za su halarci taron na Kazan, ban da Saudiyya, wadda za ta tura ministan harkokin wajenta.