A farkon wannan watan, TRT World ta tattauna baki da baki da mawaƙin Birtaniya, ɗanjarida, kuma mai fafutikar kare haƙƙin bil adama Lowkey game da yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza da kuma ra'ayinsa game da shi.
Wannan wani tsakure ne daga cikakkiyar hirar da aka naɗa a Landan, inda tattaunawar ta gudana.
Nan ba da jimawa ba za a gabatar da ita a dandalin watsa labarai na TRT World.
Rashin yin gezau a fahimtarsa da nazarinsa, Lowkey shi ne ya siffantu da cikakken "ɗan gwagwarmaya", wanda ta hanyar fasaha da sauran hanyoyin azanci a yi yunƙurin kawo kyakkyawan sauyin zamantakewa ko siyasa.
Lowkey yana hakan ne ta hanyar waƙoƙi - da ke zaburar da masu sauraro a faɗin duniya - a kan gwagwarmayar Falasdinawa ta neman adalci, da ƴanci daga mulkin dannniya na Isra'ila da haɗin bakin gwamnatocin yammacin duniya a zalincin Isra'ila.
An tace hirar domin fayyyacewa.
Yaya tunda farko ka iya haɗa hip-hop da kuma gwagwarmayar nema wa Falasdinawa ƴanci?
Lowkey: To, Ina ganin kafin na amsa wannan, ya kamata ka kalli al'ummar da na fito daga cikinta a Ladbroke Grove, Yammacin Landan. Waje ne da ake samun matasa da yawa suna da alaƙa mai ƙarfi, har da al'ummar Maroko dabam dabam, tare da Falasdinawa.
Har ila yau, waje ne inda zalincin da ake nunawa Falasdinawa a kullum yake nuna ruɗanin da ke zamaninmu.
A ɗaya ɓangaren, muna rayuwa a al'umma ce da ta ce kundin doka na Magna Carta babban misali ne na Birtaniya: ƴancin sa'anninka su yi maka hisabi, ƴancin samun hujja a kanka, da kuma ƴancin bayyana ra'ayi a dimokaɗiyyance.
Kuma abin da muka gani game da Falasdinawa shi ne duka waɗannan ƴancin an kawar da su.
Ta wannan fuskar, ina kallon waƙa a matsayin wani abu da ya zarce fasahar bayyana saƙo.
Ina mata kallon wani daidaito ne na ƙarshe inda marasa abin faɗa za su samu abin faɗa, wataƙila ba daidai da na masu galihu ba amma tana da amon da za ta iya ƙalubalantar rashin adalcin da suka aikata.
Na ga mawaƙan hip-hop da yawa sun kwanta haka a yadda suke yin waƙoƙinsu. Hakan ya ƙarfafa ni, musamman ma a kan Falasdinawa.
Ƙarfafuwar ta ƙaru a baya bayan nan, domin muna wani yanayi da za ka iya kira yanayi na suma: muryoyi da yawa, waɗanda ba dukansu ake ji ba, suna gabatar da buƙatu wa gwamnatoci cewa a yi wa Falasdinawa adalci, a mutunta rayukan Falasdinawa a matsayinsu na bil adama, amma waɗannan gwamnatocin babu abin da suke yi. Suna watsi da waɗannan muryoyin.
A fakaice zan iya dawowa fagen waƙa na rera waƙoƙin da za su sauya, da katse wannan sumar, kafin na koma duniyar da za a saki waɗannan waƙoƙin. Har wa yau, waƙa ta kasance mafaka gare ni a kodayaushe.
Akwai wani abu da ya banbanta hip-hop shi da kansa, da sauran nau'o'in fasaha, da har yake da tasiri a matsayin wata kafa ta nuna bijirewa a siyasance?
Lowkey: A kodayaushe ta kasance sadarwa ta kai tsaye ce,kamar yadda mawaƙan Larabawa suka yi amfani da waƙoƙinsu su ƙalubanci mahukunta kuma su kushe su, yayin da kuma, ta wannan hanyar za su samar da take da za su karɓu a tsakanin mutane. Ina kallon hip-hop a matsayin hanyar yin hakan, musamman ta yin suka mai ƙarfi.
Za ka iya matsa lambar siyasa ta wannan hanyar. An tunatas da ni mawaƙin Falasdinawa Mahmoud Darwish wanda ya rubuta: "Yayin da ka ƴantar da kanka a fakaice,ka tuna wasu, waɗanda suka rasa ƴancin yin magana" wani abu ne da nake sane da shi a waƙoƙina.
Kuma goyon bayana na ƙarshe yana tare da wasu ne. Ina ganin wannan ya ƙarfafa kuma ya taƙaita abin da na iya yi masana'antar waƙa, idan aka yi magana a gargajiyance.
Idan ka ji wani abu game da ƙuncin da marasa gata ke ciki, ka bai wa kanka wani kusanci da mutanen da ke goyon bayan saƙonninka na gwagwarmaya, wanda ke da matuƙar wahalar samuwa.
A lokaci guda kuma ka katse yiwuwar kaiwa wani mataki a masana'antar waƙoƙi,tunda masana'antar waƙoƙin wani tsagi ne na tsarin siyasa da tattalin arziƙi; irin sarƙaƙiyar neman iko da ke wanzuwa a cikin al'umma yana faruwa a masana'antar waƙoƙi.
Saboda haka wanda yake jin yana son nema wa marasa galihu haƙƙinsu, akwai yiwuwar ba za a yi maraba da shi ba a da'irar samun iko da nasara ba. Kai ɗanjarida ne kuma mawaƙin hip-hop.
Yaya kake iya sanin wane ɓangare ne daga cikinsu ya fi dacewa ka yi amfani da shi waje bayyana abin da ke zuciyarka?
Lowkey: Ina ganin wasu bayanan sun fi dacewa a watsa su ta hanyar aikin jarida kuma ina fahimtar haka kai tsaye.
Alal misali, idan na yi niyyar gabatar da alƙaluman da aka samu ta hanyar duba harajin wata ƙungiya da ke ɗaukar nauyin gina haramtattun matsugunan Isra'ila ko kuma kamun ƙafar siyasa game da haka, nan take - ko ko na ji a raina - na san idan aka juya shi cikin waƙa, wacce wasu za su yi amshi, ba shi ya fi dacewa ba. Irin wannan salon ba ya isar da wadataccen saƙo.
Za ka fi cim ma hakan ta hanyar waƙa. Ya fi kusanci da abin da ke sosa rai, saboda haka, yana ba ka damar taɓo ɗan'adamtakar mutum.
Tare da tunani na aikin jarida, kana taɓo hankalin mutum ne. Kana isar da bayanai, bisa ga misali, da zai iya jan hankalin makarancin ya cim ma wata matsaya.
Wannan ya zama wani abu ne mai ban sha'awa, ban da baiwata ta fasaha, a abubuwan da nake iya yi tunda wasu abubuwan na buƙatar bincike mai zurfi wajen nemo gaskiyar lamari da kuma gabatar da su a rubuce.
Amma ko waƙoƙin hip-hop ko aikin jaridan ne, ina ƙoƙarin kai wa ga mutane da yawa daidai gwargwado.,domin fallasa abin da a zahiri nuna wariya ne. Madalla, Soshiyalmidiya ya taimaka sosai wajen tabbatar da hakan.
Ƙarin mutane da dama suna sukan lamirin Isra'ila a kafofin Soshiyalmidiya. Yaya Tel Aviv za ta mayar da martani ga hakan?
Yanzu muna shiga matakin da Isra'ila ba za ta zama uwa kuma ta zama makarɓiya ba. Saboda haka a ɓangare ɗaya, masu faɗa a ji na Isra'ila cikin ƴan siyasa da sojoji da kuma jami'an tattaro bayanan sirri suna son a cim ma nasara a shirin faɗaɗa matsugunan Isra'ila.
Yanzu wannan shirin ya buƙaci Isra'ila ta ƙwace Gaza kacokan, su tura Falasdinawa sama da miliyan biyu cikin Hamadar Sinai.
Ba abu mai yiwuwa ba ne da sauƙi. Wannan wani buri ne kawai.
Har ila yau, yayin da take ƙoƙarin cim ma wannan burin, Isra'ila na rasa mutuncinta a idon jama'a, tana lalata dangantakarta - kamar yadda muke gani - hakan bai zaman mata izna ba.
Kuma, ya kamata mu san cewa,yana da muhimmanci mu fahimci maƙasudin abin da yake faruwa.
Wannan a haƙiƙanin gaskiya wata Nakba ce. Muna sheda tashin hankali a Gaza a wajen Isra'ila, wanda kuma yana da nasaba da Masallacin Birnin Ƙudus.
Alal misali, cibiyar Temple Institute, wadda tsawon shekaru Ma'aikatar Al'adu da Ma'aikatar Ilimi na Isra'ila suke ɗaukar nauyinta ta fito fili ƙarara ta yi kira da a rushe Masallacin Birnin ƙudus a maye shi da abin da ta yi imani ya wanzu dubban shekaru da suka shuɗe.
Saboda haka, wannan yaƙin a Gaza, e, ana yin shi ne da hadafin raba ɗimbin Falasdinawa da muhallansu, da kuma tsugunar da Isra'ilawa masu yawa, duk da cewa Isra'ilawa baƙi da ke zaune a Gaza su 8,000 da kaɗan ne.
Kuma don a raunana duk wani yunƙurin Falasdinawa na bijirewa duk wani yunƙurin rusa Masallacin Birnin ƙudus,har da kasuwanninsa abun ƙauna.
Ka duba a 2021,ya nuna cewa Falasdinawa a Gaza suna da rundunar da za ta iya hana wannan yunƙurin ƙwacewa da kuma rusa Masallacin Birnin ƙudus.
Ya kamata mu tuna cewa cibiyar Temple Institute ta haɗe da gwamnatin Isra'ila sosai har ta kai, a cewar wani rahoton binciken rundunar sojojin Isra'ila a 2013, gwamnatin Isra'ila ta mayar da shi a matsayin wani zaɓi shiga aikin soja.
Mata waɗanda ba sa son su shiga aikin soja za su iya shiga cibiyar a maimakon haka, su zama ƴaƴan cibiyar.
A tarihance, akwai zaman doya da manja tsakanin rundunar sojojin Isra'ila da kuma wannan ƙungiya mai kira da a lalata Masallacin Birnin ƙudus. Amma a cikin shekaru 10 zuwa 15 hakan ya canja.
Sojojin da ƙungiyoyi kamar Temple Institute suna aiki tare - a wani ɓangare na shirin aikata kisan kiyashi - a kori duk Falasdinawa daga Gaza.
A abin da ake kallo kamar shekaru aru-aru, Falasdinawa suna ta kira ga ƙasashen duniya da su saka baki, domin a dakatar da Isra'ila daga ci gaba da cutar da su - ko ta hanyar zalincin ƴansanda da azabtarwa a gidajen kaso da rushe gidajensu da kuma yi musu ruwan bamabamai na kan mai uwa da wabi,a hare haren soja da suka gabata.
Waɗanne ne daga abubuwan da suke faruwa a halin yanzu da ka yi imanin da an yi hasashen faruwarsu?
Lowkey: Mu da muka karanta tarihi kuma muka bi diddigin labarin Falasdinawa mun ga cewa ya nuna hangen da shugabannin aƙidar samar da ƙasar Yahudawa suka yi wa Isra'ila tun tuni, da ya haɗa da koran Falasdinawa.
Ya bayyana ƙarara a jawaban shugabannin aƙidar kafa ƙasar Yahudawa na farko daga David Ben- Gurion zuwa Chaim Weizmann zuwa Theodor Herzl - wanda aka fi yin amanna shi ne ya asssa aƙidar kafa ƙasar Yahudawa.
A littafinsa The Jewish State,ya ce mu, yana nuni da Isra'ilawa, za mu buƙaci my ɓatar da tarin matalautan mutane zuwa tsallaken iyaka".
Abin da yake faruwa a Gaza shi ya yi kama da ɓatar da matalautan mutane zuwa tsallaken iyaka.
Kuma abin takaici, tsawon shekaru, yayin da hakan ya ci gaba da faruwa, Isra'ila ta iya cusa kanta ba cikin wasu cibiyoyin gwamnati ba kaɗai, har ma cikin wasu sassan rayuwarsu ta al'ada. Ba Gaza kaɗai suke son jan ragamarta ba.
Ba wai ina faɗa don latsi ba. Alal misali,a masana'antar waƙoƙi,kana da wata ƙungiyar kamun ƙafa da ake kira Creative Community for Peace (CCFP). Yanzu, wannan ƙungiyar Dave Lorenzo, wanda ya fito daga Universal Music Group ne ya kafa ta.
CCFP ta bayyana kanta a matsayin mai adawa da ƙungiyar BDS [Boycott, Divestment, Sanctions] An kafa ta a matsayin ƙungiya ɗaya, kuma wata ƙungiyar a matsayin ƙungiyar kamun ƙafa - StandWithUs - wanda ofishin firaminista ke ɗaukar nauyi kai tsaye.
CCFP har wa yau tana aiki tare da ƙaramin ofishin jakadancin Isra'ila da ke Los Angeles. Kuma abu mafi muhimmanci a kan wannan, idan ka duba mutanen da ke da hannu a CCFP, za ka ga mutane ne da ke jagoranci ba a masana'antar waƙoƙi ba kawai,har ma da masana'antar fim.
Za mu iya yin gaba mu kalli daraktan Universal Music Group da aka naɗa kwanan nan: Hakim Saban. Shi ne mai samar da kuɗi mafi girma wa ƙungiyar ba da agaji ta FIDF [Friends of the Israel Defense Forces] irinsa mafi girma a tarihin ƙungiyar.
Mondoweiss ta rawaito cewa shi ne ke rubuta wa Joe Biden jawabi game da manufofin Isra'ila.
Wannan tsohon jami'in sojan Isra'ila ne, kuma mai yi wa Isra'ila kamun ƙafa,wanda a halin yanzu yake riƙe da muƙami babba a kamfanin waƙoƙi mafi girma da mahimmanci a duniya.
Za kuma ka ƙara kallon Lucian Grainge, mai tagomashi a gwamnatin Birtaniya. Makudan ina Rishi Sunak ne, mutumin da aka ɗauki hotonsa a wajen gidauniyar nema wa FIDF gudummawar kuɗi.
Shi ne CEO na Universal Music. Matarsa ce ke ɗaukar nauyin jam'iyar Conservative ta Birtaniya, da Cibiyar Henry Jackson, da ƙungiyar Zionist Federation kuma tana cikin wani kwamitin amintattu na kamfanin otel mafi girma a Isra'ila.
Saboda haka ina gani ina bayyana haka ne domin na nuna cewa akwai mutane da ba sa jin kunyar goyon bayan Isra'ila a cikin cibiyoyi na al'ada, duk da tana tafka ta'asa a kan rayukan da ba su ji ba ba su gani ba a Gaza. Wannan shi ne ainihin yanayin da muke ciki.