Isra'ila tana kai hare-hare lokaci zuwa lokaci a kan kungiyoyin da Iran take mara wa baya da kuma sojojin Syria tun lokacin da yakin basasa ya barke a 2011. / Hoto: Reuters Archive

Jiragen yakin Isra'ila sun kai hari a kusa da babban birnin Syria, a cewar kamfanin dillancin labarai na kasar SANA.

SANA, wanda ya ambato wasu majiyoyin soji suna bayyana hakan ranar Asabar, ya ce jiragen yakin sun kai hari daga Tuddan Golan da Isra'ila ta mamaye, inda suka fada yankunan da ke kusa da Damascus.

Kamfanin dillancin labaran ya ce dakarun sama na Syria sun tare rokokin da Isra'ila ta harba sannan sun kakkabo makaman Isra'ila da dama.

"Da misalin karfe 1:35 na safe (1035 GMT) a yau, Isra'ila wadda makiyiyarmu ce, ta kaddamar da hari daga yankin Syrian Golan, inda ya fada a kusa da birnin Damascus," in ji Ma'aikatar Tsaron kasar a wata sanarwa da ta fitar, ko da yake ba a bayyana ko an mutu ko jikkata ba.

Sai dai an bayyana cewa harin ya lalata wasu gine-gine.

Hare-hare irin wannan

Hare-hare ta sama da Isra'ila ta kai ranar 26 ga watan Nuwamba sun lalata filin jirgin saman Damascus awanni kadan bayan jiragen sun sake soma tashi bayan irin wannan hari da aka kai wata daya a baya.

Filayen jiragen saman Damascus da Aleppo duk sun daina aiki bayan hare-haren da Isra'ila ta kai musu a ranakun 12 da 22 ga watan Oktoba.

Isra'ila ba ta cika yin magana a game da irin wadanna hare-hare a Syria, amma ta sha nanata cewa ba za ta bari makikiyarta Iran, wadda ke goyon bayan shugaban Syria Bashar al Assad, ta karbi iko da yankin ba.

TRT World