Kungiyar ta Falasɗinu mai zaman kanta ta bayyana cewa kamen na baya-bayan nan ya sa yawan Falasɗinawan da aka tsare tun ranar 7 ga watan Oktoba ya kai 3,365. / Hoto: AFP / Photo: Reuters

1024 GMT — Isra'ila ta ce sojojinta sun daƙile wani hari daga Labanon

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta dakile wani hari ta sama da ya tsallaka daga Lebanon, a wani lamari da ya dagula yanayi zaman lafiyar da ake samu a kan iyakar tun bayan da kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas da Isra'ila suka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta wucin gadi.

Shaidu na Reuters sun ji ƙarar tashin bama-bamai a yankin kudu maso gabashin Lebanon. Kawo yanzu dai babu wanda ya ɗauki alhakin duk wani hari daga kasar Labanon ɗin.

Isra'ila da kungiyar Hizbullah ta Lebanon sun shafe makonni suna musayar wuta a kan iyakar kasar. Sauran kungiyoyi da suka hada da Hamas da kungiyar Jihad Islama ta Falasdinu su ma sun kaddamar da hare-hare daga Lebanon kan Isra'ila a lokacin rikicin.

1130 GMT — Sojojin Isra'ila sun sake kama Falasdinawa 40 a Yammacin Kogin Jordan

Rundunar sojin Isra'ila ta tsare aƙalla Falasɗinawa 40 a wani samame da ta kai Yammacin Kogin Jordan da safiyar ranar Alhamis, a cewar Ƙungiyar Fursunoni ta Falasɗinawa.

Kungiyar ta Falasɗinu mai zaman kanta ta bayyana cewa kamen na baya-bayan nan ya sa yawan Falasɗinawan da aka tsare tun ranar 7 ga watan Oktoba ya kai 3,365.

Tashin hankali na ƙaruwa a Yammacin Kogin Jordan a yayin da sojojin Isra'ila ke kai hare-hare Zirin Gaza tun bayan harin ba-zatan da Hamas ta kai wa Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba.

1200 GMT — An kashe mutum uku a harin da aka kai a Gabashin Birnin Ƙudus

Aƙalla mutum uku ne suka mutu sannan shida suka jikkata, ciki har da biyun da ke cikin wani mummunan yanayi, a wani harbe-harbe da aka yi a yankin Gabashin Birnin Kudus da Yahudawa ƴan kama wuri zauna suka mamaye.

'Yan sanda sun ce a ranar Alhamis din nan an kashe mutum biyu da ake zargi da hannu a harbe-harben a nan take bayan harin da aka kai a kusa da tashar motar bas da ke Yammacin Birnin Kudus, inda babu shingayen binciken ababen hawa da ke gadin hanyar shiga birnin.

‘Yan ta’adda biyu ne suka isa a mota, daya daga cikinsu dauke da M-16, ɗaya kuma ɗauke da bindiga,” inda suka buɗe wuta, kamar yadda shugaban ‘yan sandan Kudus, Doron Torgeman ya shaida wa manema labarai a wurin.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Magen David Adom ta ce daya daga cikin waɗanda abin ya shafa wata mace ce mai shekara 24 da haihuwa.

Harin na zuwa ne jim kadan bayan da aka tsawaita wa'adin tsagaita wuta a Zirin Gaza tsakanin mayaƙan Falasdinawa da Isra'ila na tsawon kwanaki bakwai, kafin cikar wa'adin.

0455 GMT — Isra'ila da Hamas sun amince a kara wa'adin tsagaita wuta da kwana daya

Isra'ila da kungiyar Hamas mai rajin kare hakkin Falasdinawa sun amince su tsawaita yarjejeiyar tsagaita zuwa karin kwana daya.

Kazalika sojojin Isra'ila sun ce za a ci gaba da mutunta yarjejeniyar "bisa kokarin masu shiga tsakani na ci gaba da ganin an saki karin mutanen da aka yi garkuwa da su, kuma a kan sharudan da aka yarda da su."

Kasar Qatar wadda ke shiga tsakani ta tabbatar da cewa Isra'ila da Hamas sun amince su tsawaita wa'adin yarjejeniyar.

0200 GMT — An gaya wa mayakan Hamas su sanya damara don ci gaba da yaki

Kasashen duniya na matsa lamba kan Isra'ila da Hamas domin su tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta bayan sun yi musayar karin fursunoni sannan an bar karin kayan agaji sun shiga yankin Gaza da aka mamaye.

Sai dai "Majalisar Yaki" ta Isra'ila ta kammala taronta ba tare da cim ma matsaya kan tsawaita yarjejeniyar ba, kamar yadda TRT World ta fahimta. Wasu kafofin watsa labarai na Isra'ila sun ambato majiyoyi suna cewa "jerin sunayen karin mutanen da Hamas ta nemi a sako bai cka sharudan" Isra'ila ba."

Yarjejeniyar tsagaita wutar za ta daina aiki ne da misalin karfe 7 na safe a agogon Gaza, wato karfe 5 a agogon GMT.

Sashen soji na kungiyar Hamas ya shaida wa mayakansa su daura damarar komawa yaki da Isra'ila idan ba a tsawaita yarjejeniyar ba.

"Al-Qassam Brigades yana umartar dakarunsa su kasance cikin shirin ko-ta-kwana a awannin karshe na karewar yarjejeniyar," in ji sanarwar ya fitar. An bukaci mayaka su shiga cikin "damara har sai an fitar da sanarwa a hukumance game da tsawaita yarjejeniyar tsagaita wutar," kamar yadda sanarwar ta kara da cewa.

Mayakan Hamas suna sallah bayan sun mika Isra'ilawa da suka saka ga kungiyar International Red Cross./Hoto:Reuters

0149 GMT — China ta bukaci a samar da kasashe biyu

China ta yi kira ga Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya shirya wani jadawali da zai kai ga samar da kasashe biyu masu cin gashin kansu tsakanin Isra'ila da Falasdinu domin kawo karshen rikicinsu.

Ma'aikatar Harkokin Wajen China ce ta gabatar da wannan shawara a rubuce kan rikici Gaza, a yayi da kasar ta karbi jagorancin Kwamitin -- wanda ake yin karba-karba -- a watan Nuwamba.

Akwai bukatar Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya kara kaimi wurin tattaunawar diflomasiyya da kuma sake duba batun samar da kasashe biyu masu cin gashin kansu sannan ya hada taron kasashen duniya da zai samar da "kwakkwaran tsari mai amfani" na shawo kan rikicin, in ji takardar da China ta gabatar.

Ta yi kira ga mambobi 15 na Kwamitin su saurari kiraye-kiraye kasashen duniya na tabbatar da tsagaita wuta a yakin.

0155 GMT — Fitacciyar mai fafutuka Ahed Tamimi na cikin Falasdinawa da Isra'ila ta saka

Fitacciyar Bafalasdiniyar nan mai fafutuka Ahed Tamimi na cikin mutum 30 da Isra'ila ta saka a yarjejeniyar musayar fursunoni tsakaninta da Hamas, a cewar jami'an Isra'ila da na Falasdinu.

A farkon watan nan dakarun Isra'ila suka kama Tamimi, wadda ake yi wa kallon gwarzuwa a Gabar Yamma da Kogin Jordan tun tana matashiya, bayan an zarge ta da tunzura mutane su yi tarzoma.

Mahaifiyarta ta musanta zargin tana mai cewa an yi shi ne bisa wani sakon bogi a shafukan sada zumunta.

Hukumar kula da gidajen yarin Isra'ila ta wallafa sunayen Falasdinawa da ta saka ranar Alhamis da safe a shafinta na intanet ciki har da Tamimi.

TRT Afrika da abokan hulda