Lahadi, 28 ga watan Yuli, 2024
0801 GMT — Sojojin Isra’ila sun jefa bama-bamai kan ƙauyuka da birane a Lebanon, kwana guda bayan Isra’ilar ta zargi Hezbollah da kai hari Majdal Shams da ke Tuddan Golan da Isra’ilar ta mamaye.
Jiragen yaƙi sun yi luguden wuta a wajen biranen Aabbassiyeh, Tayr Debba da Toura da ke gundumar Tyre.
Haka kuma jiragen yaƙin sun kai hare-hare a Burj al Shemali da Tayr Harfa wanda hakan ya jawo asarar rayuka da dukiyoyi.
Hukumomin Isra'ila sun ce akalla mutum 12 ne suka mutu sannan wasu 35 suka jikkata sakamakon harin makami mai linzami da aka kai kan garin Druze da ke Majdal Shams a arewacin Tuddan Golan.
Sojojin Isra'ila sun zargi Hezbollah da kai harin, amma kungiyar ta Lebanon ta musanta kai harin.
0038 GMT — Sojojin Isra'ila sun kai samame a sansanin 'yan gudun hijira na Balata da ke gabashin Nablus a arewacin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan ranar Asabar da maraice a karo na huɗu cikin awanni 24.
Kamfanin dillancin labarai na Falasɗinu, Wafa, ya ruwaito cewa dakarun Isra'ila sun kutsa cikin sansanin inda suka buɗe wuta, tare da yin amfani da gwanayen harbi na ɓoye da kuma manyan motocin rusa gine-gine.
Masu fafutuka a shafukan sada zumunta sun yi ta wallafa bidiyoyin da ke nuna ƙarin dakarun Isra'ila suna shiga cikin sansanin tare da jin ƙarar harbe-harbe, inda suka yi iƙirarin cewa ana yin ba-ta-kashi ne tsakanin ƙungiyoyin Falasɗinawa da sojojin na Isra'ila.
Sojojin sun fice daga sansanin da tsakar dare bayan sun shafe awanni suka cin zarafin jama'a tare da kashe aƙalla mutum biyu da jikkata gommai, a cewar ganau da kuma hukumomin kiwon lafiya na Falasɗinu.
A yayin da Isra'ila ke yaki a Gaza, a gefe guda kuma tana ci gaba da kai samame a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, lamarin da ya kai ga mutuwar mutum 592 tare da jikkata mutum 5,400, a cewar alƙaluma daga hukumomin Falasɗinu.
An daɗe ana tayar da jijiyoyin wuya a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da Gabashin Birnin Ƙudus da aka mamaye, a yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare a Gaza waɗanda suka yi sanadin mutuwar Falasɗinawa kusan 39,300 tun daga ranar 7 ga watan Oktoba.