Sisi na Masar da shugaban CIA sun tattauna batun sasanta rikicin Gaza a Alkahira  / Hoto: AFP

1155 GMT — Sisi na Masar da shugaban CIA sun tattauna batun sasanta rikicin Gaza a Alkahira

Shugaban Masar Abdel Fattah el Sisi ya gana da daraktan hukumar leƙen asiri ta CIA William Burns a birnin Alkahira, inda tawagogin Amurka da na Isra'ila suka tattauna kan yunkurin tsagaita wuta a Gaza.

Ofishin Sisi ya ce mutanen biyu sun tattauna kan sabbin abubuwan da suka faru a yunkurin hadin gwiwa na cimma matsaya da tsagaita wuta a Gaza, inda sojojin Isra'ila da ke samun tallafin tankokin yaki da jiragen yaki suka ƙara ƙaimi a yankin Falasdinu.

Masu shiga tsakani na Masar da Qatar sun shafe watanni suna tattaunawa da nufin cimma matsaya da yarjejeniyar musayar fursunoni a Zirin Gaza.

1004 GMT — Yawan Falasɗinawan da suka mutu a hare-haren Isra'ila a Gaza ya kai 38,243

Akalla Falasdinawa 38,243 ne suka mutu sannan 88,033 suka jikkata a hare-haren da sojojin Isra'ila suka kai a Gaza tun ranar 7 ga watan Oktoba, in ji ma'aikatar lafiya a yankin da aka yi wa kawanya.

0700 GMT — Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 16 a sabon luguden wutar da ta yi a Gaza

Falasɗinawa aƙalla 16 sun mutu sannan gomman suka jikkata sakamakon jerin hare-hare ta sama da Isra'ila ta kai a sassa daban-daban na Gaza da daddare.

Wata majiya daga asibiti ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu Agency cewa Isra'ila ta kashe mutum bakwai a harin da ta kai gidansu a sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar Gaza.

Kazalika wani hari ta sama da jirgin yaƙin Isra'ila ya kai ya kashe iyalai shida na wani mutum mai suna Mhanna a yankin Al-Jalaa sannan an kashe wasu mutum uku a hari ta sama da jirgin yaƙin Isra'ila ya kai a yankin Lababidi na Birnin Gaza, a cewar kamfanin dillancin labarai na Falasɗinu, Wafa.

A gefe guda, ma'aikatan ceto sun ciro gawar wani yaro da ya maƙale a cikin ɓaraguzai tare da wasu da suka jikkata a gidansu a gabashin Birnin Gaza, a cewar Wafa.

Ranar Litinin rundunar sojin Isra'ila ta umarci mutane a faɗin Birnin Gaza su fita daga gidajensu a yayin da ta kai samame a gabashi da kudancin birnin.

2119 GMT — Majalisar Ɗinkin Duniya ta ba da bayanin mummunar tasirin yaƙin Isra'ila a birnin Gaza

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce wa'adin baya-bayannan da Isra'ila ta bayar da ya tilasata wa Falasɗinawa ficewa daga wani ɓangare na birnin Gaza da aka mamaye ya shafi fiye da makarantu 60 inda Falasɗinawan da yaƙi ya raba da gidajensu suke samun mafaka, tare da wasu abitoci biyu da suke aiki rabi-da-rabi da wuraren karɓar magani shida da cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko guda biyu.

Su ma jami'an ba da agaji sun ba da rahoton cewa ma'aikata da marasa lafiya sun tsere daga asibitoci a wuraren da Isra'ila ta yi wa barazana da ma kusa da su, kuma an sake tilasta wa mutanen da dama da suka bar gidajensu sake guduwa a yanzu, kamar yadda mai magana da yawun Majalisar Ɗinkin Duniya Stephane Dujarric ya bayyana.

Ofishin na ba da agaji ya kuma ba da rahoton cewa luguden wuta, da lalata hanyoyi, da rashin iya zuwa wurare da rashin doka da oda na ci gaba da hana zirga-zirga a kan babbar hanyar kai agaji daga mashigar Kerem Shalom [Karam Abu Salem] zuwa Khan Younis, sannan zuwa Deir al-Balah," a cewar Dujarric.

Ya ce hakan ya haifar da mummunan ƙarancin abinci, ya kuma rage abincin da ake rabawa a tsakiya da kudancin Gaza a watan jiya, da kuma ƙaruwar fargabar lalacewar kayan agajin, musasmman abinci saboda zafin rana.

"A yanzu gidajen burodi uku daga 18 da abokan aikinmu masu agaji suke tallafawa ne kawai suke aiki a Gaza, dukkansu a Deir al-Balah," kamar yadda Dujarric ya bayyana. "Yayin da rashin makamashi ya tilasta wa gidajen burodin da suke aiki kaɗan suka dakatar da aiki baki ɗaya."

Maysa Saleh, jami'in ilimi na ƙungiyar ba da agaji ta Norwegian Refugee Council a Deir al-Balah ya ce "kusan babu agajin da ya iso tun makon jiya ko makamancin haka," sannan "abinci shi ne babban abin da aka fi damuwa da shi."

An kai Falasɗinawan da aka jikkata ciki har da yara, Asibitn Indonesia bayan harin Isra'ila a yankin Tuffah na birnin Gaza. / Hoto: AA
TRT World