Bayan harin da aka kai a watan Oktoba Haliva ya dora laifin rashin hana aukuwar harin akansa. / Hoto: Reuters      

Rundunar sojojin Isra'ila ta ce shugaban hukumar leƙen asirinta ya yi murabus saboda gazawarsa wajen hana harin ba- zata da kungiyar Hamas ta kai kasar a ranar 7 ga watan Oktoba, wanda ya keta kariyar tsaron Isra'ila.

Aharon Haliva, shugaban hukumar leken asirin sojin Isra'ila, ya zama jigo na farko a Isra'ila da ya sauka daga mukaminsa a ranar Litinin, bayan harin, wanda Isra'ila ta yi ikirarin kashe mutane 1,200, tare da yin garkuwa da wasu kusan mutane 250.

“Manjo Janar Aharon Haliva, tare da goyon bayan babban hafsan hafsoshin sojin kasar, ya bukaci ya yi murabus, biyo bayan alhakin da ya rataya a wuyansa a matsayinsa na shugaban hukumar leken asiri kan abubuwan da suka faru a ranar 7 ga watan Oktoba,” a cewar rundunar sojin Isra'ila.

"An yanke shawarar cewa Manjo Janar Aharon Haliva zai ajiye mukaminsa kuma zai yi ritaya daga rundunar leƙen asirin sojin Isra'ila IDF, da zarar an nada magajinsa cikin tsari da ƙwarewa."

'Ina dauke da wannan baƙar ranar tare da ni'

A takardar ajiye aikinsa, Haliva ya dauki alhakin gaza daƙile ko hana harin.

"A ranar Asabar, 7 ga Oktoba, 2023, Hamas ta kai wani mummunan harin ba-zata a kan Isra'ila," kamar yadda ya rubuta a cikin wasikar da aka rundunar ta raba wa ƴan jarida.

“Sashen rundunar leken asirin da ke karkashin ikona ba su sauke nauyin da aka dora mana ba... tun daga nan nake dauke da wannan bakar rana a tare da ni, dare da rana, kuma zan ci gaba da rike kunciin yakin a raina."

A wata sanarwa da rundunar sojin Isra'ila ta fitar ta ce babban hafsan sojojin kasar ya amince da bukatar Jaliva na yin murabus tare da gode masa bisa ga aikin da ya yi.

Ajiye aikin nasa na iya buɗe kofa ga wasu manyan jami'an tsaron Isra'ila su ɗauki laifin rashin dakile ko hana kai harin da kana su aije mukaminsu.

TRT World