Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya miƙa ta'aziyyarsa ga Tehran bisa rasuwar shugaban Iran Ebrahim Raisi da abokan tafiyarsa a wani hatsarin jirgin helikwafta.
An sanar da mutuwar Shugaba Raisi da Ministan Harkokin Wajen ƙasar Hossein Amirabdollahian da abokan aikinsu ne a safiyar Litinin, bayan wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu.
"Ina mika ta'aziyyata ga takwarana kuma ɗan'uwana, shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Ibrahim Raisi, wanda ya rasu cikin mummunan hatsarin jirgin Helikwafta," a cewar saƙon Shugaba Erdogan da aka wallafa a shafin X a ranar Litinin.
Erdogan ya miƙa ta'aziyyarsa ga Jagoran Addini na Iran Ali Khamenei, da iyalan Raisi da al'umma da gwamnatin ƙasar da kuma sauran iyalan waɗanda hatsarin ya shafa baki ɗaya.
"A matsayina na abokin aiki wanda na shaida ƙoƙarinsa na tabbatar da zaman lafiyar al'ummar Iran da yankinmu, ina tunawa da Shugaba Raisi cikin girmamawa da jinjinawa," in ji Erdogan.
Shugaba Erdogan ya ba da tabbacin cewa, Turkiyya za ta ci gaba da goyon bayan maƙwabciyarta Iran a wannan mawuyacin lokaci, kamar yadda ta yi a lokuta da dama a baya.
Haɗarin dai ya haifar da kaɗuwa a yankin, inda mutane da dama ke jimamin rashin shugaban na Iran da sauran jami'an dake cikin jirgin.
Ta'aziyyar ministan harkokin wajen Turkiyya
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan, a wani taron manema labarai na haɗin gwiwa da takwaransa na Pakistan a Islamabad, a ranar Litinin shi ma ya jajanta aukuwar lamarin, yana mai cewa ''abin takaici da kuma baƙin ciki ne samun labarin mutuwar shugaba Iran da ministan harkokin wajen kasar. Muna cikin jimami da damuwa irin wacce 'yan 'uwanmu na iran ke ciki.''
Jim kadan bayan aukuwar haɗarin a yankin arewa maso yammacin lardin Azarbaijan na kasar Iran a yammacin Lahadi, Turkiyya ta tura da dukkan wasu muhimman kayan aiki da za su taimaka wajen ayyukan bincike da ceto a wurin, in ji shi.
Da safiyar ranar Litinin ne jirgin Bayraktar Akinci mara matuƙi na Turkiyya ya gano wani wuri mai zafi da ake zargin anan ne jirgin saman mai saukar ungulu ɗauke da shugaban Iran Raisi ya yi hatsari, kana ya yi saurin sanar da hukumomin Iran da suke haɗin gwiwa, a cewar rahoton da kamfanin dillacin labaran Anadolu ya fitar.
Bayan gudanar da bincike da aikin ceto a wurin, an gano gawawwaki cikin har da ta shugaban Iran da na ministan harkokin wajen kasar da sauran mutane, a cewar kafar talabijin ta ƙasar ta Iran.
Raisi ya kasance a Azerbaijan da sanyin safiyar Lahadi don ƙaddamar da wata madatsar ruwa tare da Shugaban Azerbaijan Ilham Aliyev. Madatsar ruwan dai ita ce ta uku da ƙasashen biyu suka gina a kan Kogin Aras.
Ziyarar ta zo ne duk da taɓarɓarewar alaƙa tsaƙanin ƙasashen biyu, ciki har da harin bindiga da aka kai ofishin jakadancin Azarbaijan da ke Tehran a shekarar 2023, da kuma hulɗar diflomasiyyar Azarbaijan da Isra'ila, wacce Iran mai bin tafarkin Shi'a ke kallonta a matsayin babbar makiyarta a yankin.