1358 GMT — Sabbin hare-haren Isra'ila sun kashe gomman mutane 'yan gida daya a Gaza
An kashe da raunata mutane da dama 'yan gida ɗaya a wasu hare-hare biyu da Isra'ila ta kai a ranakun Alhamis da Juma'a, a kan gidajensu a garin Jabalia da ke arewacin Gaza.
Munir Al Bursh, babban daraktan Ma'aikatar Lafiya ta Falasdinu a Gaza, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa ya samu rauni, kuma an kashe 'yarsa.
Bugu da kari, wasu daga cikin iyalansa na Al Bursh da kuma dangin ɗan'uwansa sun sami raunuka sakamakon wani harin da Isra'ila ta kai kan gidan ɗan'uwansa da ke Jabalia a yammacin ranar Alhamis.
A wani harin da aka kai ta sama, majiyoyin likitocin Falasdinawa sun shaida wa wakilin Anadolu cewa an kashe Falasdinawa 16, sannan wasu kusan 50 suka jikkata, kuma dukkansu 'yan gidan Al Bursh ne.
Wannan ya faru ne sakamakon harin da aka kai ta sama da aka kai a gidan iyali a Jabalia.
1055 GMT — An juya akalar jiragen ruwa 170, an kuma tsayar da 35 saboda hare-haren Houthi a Bahar Maliya
Kamfanin jigilar kayayyaki na Amurka Flexport Inc ya ce an karkatar da jiragen ruwa kusan 170 daga Mashigin Bab el Mandeb da ke Bahar Maliya kuma an dakatar da jiragen ruwa 35, suna jiran umarni daga kamfanonin da suke yi wa aiki.
A cewar wata sanarwa da kamfanin da ke San Francisco ya fitar, kimanin jiragen ruwa 170 masu ɗauke da kwantena aka mayar da su zuwa kasashen Afirka, yayin da wasu jiragen ruwa 35 suka tsaya cik sakamakon hare-haren da aka kai a Tekun Bahar Maliya.
A gefe guda kuma, kungiyar Houthi a Yaman ta ci gaba da yin barazanar kai hare-hare kan jiragen ruwa da ke da alaka da Isra'ila da ke ratsa mashigar tekun da ke kudu da Tekun Bahar Maliya, don goyon bayan Falasdinawan da ake ta yi wa ruwan bama-bamai a Gaza.
0509 GMT — Isra'ila ta kashe Falasdinawa 20,057 a Gaza tun 7 ga watan Oktoba
Adadin Faladinawan da Isra'ila ta kashe ya kai 20,057, a cewar Ma'aikatar Lafiya ta Falasdinu ranar Juma'a.
An jikkata akalla mutum 53,320 a hare-haren da Isra'ila ta kai yankin tun daga 7 ga watan Oktoba, in ji ma'aikatar.
"An kashe akalla mutum 390 sannan aka jikkata mutum 734 a awanni 48 da suka gabata inda aka katse hanyoyin sadarwa na Zirin Gaza," a cewar sanarwar da ma'aikatar ta fitar.
0054 GMT — An sake jinkirta kaɗa ƙuri'ar MDD yayin da Isra'ila ta yi ruwan bama-bamai a Gaza
Majiyoyin diflomasiyya sun ce Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya sake yin watsi da kaɗa ƙuri'a kan ƙudurin da aka jinkirta kan yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza.
Dage kaɗa ƙuri'ar da aka yi a yau Juma'a ya zo ne a daidai lokacin da Amurka da ta dinga adawa da shawarwari da dama a lokacin ƙudurin, ta ce a shirye take ta ba da goyon baya a yadda take a halin yanzu.
Majalisar Dinkin Duniya ta shirya kaɗa ƙuri'a da aka daɗe ana jinkirtawa kan wani sabon kuɗuri na dakatar da yaƙin ta wata hanya, wadda za ta ba da damar ƙara kai agajin jinƙai.
0110 GMT — Mun shirya don kada ƙuri'a kan ƙudurin Gaza
Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a shirye yake ya kaɗa ƙuri'a kan daftarin kudirin ba da agajin jinƙai a Gaza, in ji jakadiyar Amurka a MDD.
"Ina so in gaya muku cewa mun yi aiki tuƙuru da himma a cikin makon da ya gabata tare da ƙasar UAE da Masar, don samar da wani ƙuduri da za mu iya marawa baya. Kuma muna da wannan ƙuduri a yanzu.
"A shirye muke mu kaɗa ƙuri'a a kai," kamar yadda Linda Thomas-Greenfield ta shaida wa manema labarai bayan wani taron majalisar dokoki na sirri da aka yi kan halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya.
Ta ce wani ƙuduri ne da zai kawo agaji ga mabuƙata.
2155 GMT — Fiye da kasashe 20 sun shiga gamayyar kawancen hadin gwiwa na Bahar Maliya
Sama da kasashe 20 ne suka shiga cikin kawancen da Amurka ke jagoranta domin kare jigilar jiragen ruwa a Tekun Bahar Maliya daga hare-haren 'yan tawayen Houthi na Yemen, kamar yadda Ma'aikatar Tsaron Amurka Pentagon ta bayyana.
'Yan tawayen Houthi sun sha kai hare-hare kan jiragen ruwa a muhimmin titin jiragen ruwa tare da kai hare-hare na goyon bayan Falasdinawa a Gaza, inda Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare kan fararen hula.
Mai magana da yawun Pentagon, Major General Pat Ryder ya shaida wa manema labarai cewa, "Mun sami sama da kasashe 20 da suka sanya hannu kan shiga cikin kawancen."
Ryder ya ce Houthis suna "kai hari ga walwalar tattalin arziki da ci gaban al'ummomin duniya," tare da zama "'yan fashi a kan babbar hanyar kasa da kasa wato Bahar Maliya."
Dakarun hadin gwiwa za su "yi aiki a matsayin sintiri iri-iri na babbar hanya, suna sintiri a Tekun Bahar Maliya da Tekun Aden don mayar da martani - da kuma taimakawa kamar yadda ya cancanta - tasoshin kasuwanci da ke jigila a wannan muhimmiyar hanyar ruwa ta kasa da kasa," in ji shi, yana mai kira ga Houthis da su daina kai hare-haren.