Adadin waɗanda aka kashe a Gaza ya kai 41,118 yayin da Isra'ila ke ci gaba da kashe Falasɗinawa / Hoto: AA / Photo: Reuters

Alhamis, 12 ga Satumban 2024

1415 GMT — Akalla Falasdinawa 21 ne aka kashe a wasu sabbin hare-hare da Isra’ila ta kai a Zirin Gaza da ke fama da yaki kamar yadda majiyoyin lafiya suka bayyana.

Wata majiyar kiwon lafiya ta ce wani jirgin mara matuki na Isra'ila ya kai hari kan fararen hula a unguwar Zeitoun a kudu maso gabashin birnin Gaza, inda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu tare da jikkata wasu da dama.

Hakazalika majiyar ta ce wasu karin mutane hudu sun rasa rayukansu kana wasu bakwai kuma suka jikkata a wani harin da jiragen yaki mara matuki suka kai a yammacin birnin Gaza.

Wata sanarwa da ma'aikatar tsaron farin kaya ta Isra'ila ta fitar ta ce wani harin da jiragen yakin kasar Isra'ila suka kai kan wani gida a unguwar Zeitoun, inda ya kashe mutane 5 ciki har da yara biyu.

Sanarwar ta kara da cewa, an kashe karin mutane uku a wani harin da aka kai kan wani gida a sansanin 'yan gudun hijira na Jabalia da ke arewacin Gaza.

1050 GMT — Adadin waɗanda aka kashe a Gaza ya kai 41,118 yayin da Isra'ila ke ci gaba da kashe Falasɗinawa

Hare-haren Isra'ila sun kashe aƙalla ƙarin Falasɗinawa 34 a Gaza, abin da ya kai adadin waɗanda suka mutu tun daga 7 ga Oktoba zuwa 41,118, a cewar Ma'aikatar Lafiya ta yankin.

Wata sanarwar ma'aikatar ta ƙara da cewa an jikkata fiye da wasu mutanen 95,125 a hare-haren da ake ci gaba da kaiwa.

"A cikin sa'o'i 24, Sojojin Israi'ila sun kashe mutane 34 sun kuma jikkata wasu 96 a kashe-kashe na ƙare dangi da suke yi wa iyalai," a cewar ma'aikatar.

Ta ƙara da cewa "Mutane da dama har yanzu suna kwance a ƙasan ɓaraguzai da kuma gefen hanyoyi kasancewar masu aikin ceto ba sa iya kaiwa gare su."

0843 GMT — Turkiyya za ta binciki kisan da aka yi wa mai ayuakan jin ƙai 'yar gwagwarmaya a Gaɓar Yamma

Turkiyya na binciken kisan da aka yi wa Ba'amurkiya kuma Baturkiya 'yar gwagwarmaya Aysenur Ezgi Eygi yayin wata zanga-zanga a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da sojojin Isra'ila suka mamaye, kamar yadda ministan shari'a ya bayyana, yana mai cewa Ankara za ta matsa wa Majalisar Ɗinkin Duniya kan ta ɗauki mataki nan take.

"Turkiyya ta fara bincike," a cewar Ministan Shari'a Yilmaz Tunc.

"Za mu yi aiki don tabbatar da cewa Wakilin Majalisar Ɗinkin Duniya na Musamman kan Kisan Zalinci ya ɗauki mataki nan-take, sannan a kafa wani kwamitin bincike mai zaman kansa ya kuma fitar da rahoto," a cewarsa.

TRT World