Isra'ila ta kashe Falasdinawa sama da 14,128, ciki har da yara 5,840 da mata 3,920, a cewar hukumomin lafiya a yankin. Hoto: AA

Kamfanin dillancin labarai na KAN ya ce rundunar sojin Isra'ila na shirin yin amfani da yarjejeniyar tsagaita wuta don sake shirya dakarunta a shirye-shiryen fadada hare-hare ta kasa a kudancin Gaza.

Rundunar sojin Isra'ila ta amince da yarjejeniyar musayar wadanda aka yi garkuwa da su da kuma tsagaita wuta na wucin-gadi da kungiyar Falasdinawa ta Hamas a Zirin Gaza, kamar yadda kafafen yada labarai na cikin gida suka ruwaito a ranar Talata.

"Rundunar soji na shirin yin amfani da tsagaita wuta domin sake shirya dakarunta a shirye-shiryen fadada kai hare-haren ta kasa zuwa kudancin Gaza," a cewar kafar yada labarai ta KAN.

A cewar kafar yada labaran, yarjejeniyar da aka cimma ta hada da tsagaita wuta na kwanaki hudu, da kuma sakin wasu ‘yan Isra’ila 50 da Hamas ke garkuwa a musayar Falasdinawa 150 da ke gidajen yarin Isra’ila.

Isra'ila ta yi kiyasin cewa akalla Isra'ilawa 239 ne Hamas ke tsare da su bayan harin da aka kai kan iyaka a ranar 7 ga watan Oktoba.

Isra'ila ta kai hare-hare ta sama da ta kasa a Zirin Gaza bayan harin ba-zata na Hamas, inda ta kashe Falasdinawa sama da 14,128, ciki har da yara 5,840 da mata 3,920, a cewar hukumomin lafiya a yankin.

Dubban gine-gine, da suka hada da asibitoci da masallatai da majami'u aka rusa ko lalata a hare-haren da Isra'ila ta kai ta sama da ta kasa kan yankin da aka yi wa awanya.

Adadin wadanda suka mutu a Isra'ila, ya kai kusan 1,200, a cewar alkaluman hukuma.

TRT World