Alhamis, 5 ga Disamban 2024
1444 GMT — Kungiyar gwagwarmayar Falasdinu ta Hamas ta ce rahoton da Amnesty International ta fitar na zargin Isra'ila da kisan kiyashi a yankin Falasdinu, kira ne da a dauki mataki a duniya.
Rahoton wani sabon sako ne ga kasashen duniya...a kan bukatar daukar matakin kawo karshen wannan kisan kiyashi da aka shafe sama da kwanaki 400 ana yi, in ji kungiyar a cikin wata sanarwa.
Masar ta bayar da shawarar sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza
Masar ta bayar shawarar kafa sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza wadda ta ƙunshi batun tsagaita wutar ta kwanaki 45 zuwa 60 tare da buɗe mashigar Rafah, kamar yadda kafar watsa labarai ta Isra’ila ta ruwaito a ranar Alhamis.
Yarjejeniyar ta kuma ƙunshi sakin ‘yan Isra’ila waɗanda ake riƙe da su domin musayar Falasɗinawan da aka kama da kuma batun ƙara adadin motocin kai agaji cikin Gaza zuwa 350 a duk rana, kamar yadda kafar watsa labarai ta Isra’ila ta Channel 12 ta ruwaito.
“Zuwa yanzu ba a kammala amincewa da abubuwan da ke ƙunshe a cikin yarjejeniyar ba, sai dai za a iya fahimtar cewa za a iya cim ma wannan yarjejeniyar a mataki bayan mataki, inda matakin na farko zai ɗauki kimanin wata guda zuwa wata ɗaya da rabi ko wata biyu,” kamar yadda kafar watsa labaran ta ruwaito.
0632 GMT — Dakarun Isra'ila sun karya ƙarin yarjeniyoyi 12 na tsagaita wuta da suka ƙulla da Lebanon a makon jiya, a cewar kamfanin dillancin labarai na Lebanon.
Ya ce Isra'ila ta karya yarjejeniyar ce sakamakon hare-haren da ta kai a gundumomin Tyre, Marjayoun da Bent Jbeil da ke kudancin Lebanon da kuma birnin Beirut.
Abubuwan da Isra'ila ta yi sun haɗa da lalata gidaje da luguden wuta da shawagin jiragen yaƙinta ta saman ƙasar Lebanon da buɗe wuta a wasu wurare.
Lebanon ta ce Isra'ila ta keta yarjejeniya sau 129 tun da suka amince su tsagaita wuta domin kawo ƙarshen yakin da suka kwashe watanni 14 suna fafatawa da Hezbollah.
1835 GMT — Harin da Isra'ila ta kai a wani sansanin 'yan gudun hijira a Gaza ya halaka aƙalla mutum 21
Wani jami'in lafiya na Falasdinu ya ce akalla mutane 21 ne suka mutu sakamakon harin da Isra'ila ta kai kan wani sansanin da ke dauke da 'yan gudun hijira a Gaza.
Atif Al-Hout, daraktan Asibitin Nasser da ke kudancin birnin Khan Younis, ya ce akalla mutane 28 ne suka jikkata sakamakon harin.
Akalla gawarwakin mutane 15 ne suka isa asibitin, amma ba a san ainihin yawansu ba, domin da yawa daga cikin gawarwakin wadanda suka mutu sun dagargaje, wasu babu wasu sassan jikinsu wasu kuma sun ƙone sosai.
Harin ya afku ne a yankin Mawasi, wani sansani da ke bakin teku da ke dauke da dubban mutanen da suka rasa matsugunansu a kusa da birnin Khan Younis na kudancin kasar.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce jiragenta sun kai hari kan yankunan Hamas, amma ba zai yiwu a kai ga tabbatar da ikirarin na Isra'ila ba.
1846 GMT — Sojojin Isra'ila sun dawo da gawar wani daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su
A wata sanarwa da rundunar sojin Isra'ila ta fitar ta ce ta kwato gawar Ita Svirsky wanda aka yi garkuwa da shi a ranar 7 ga watan Oktoban 2023.
A wata sanarwa da kungiyar iyalan wadanda aka yi garkuwa da su ta fitar, ta ce mayar da "gawar Itay don binne ta a Isra'ila ya bai wa danginsa wani dan saukin ƙuncin rai".
1807 GMT — Harin Isra'ila ya kashe Falasdinawa 47 a yankin
Likitocin Falasdinawa sun ce wasu hare-haren da Isra'ila ta kai ta sama sun kashe akalla mutane 47 a yankin.
Mazauna yankin sun ce tankokin yaki sun ci gaba da kutsawa kwana guda bayan da sojojin Isra'ila suka ba da sabbin umarnin kwashe mutane a wajen.
Yayin da harsasai suke faɗawa a kusa da wuraren zaman mutane, iyalai sun bar gidajensu inda suka nufi yamma zuwa yankin da aka keɓe a matsayin na jinƙai na Al Mawasi.