Laraba, 27 ga watan Nuwamba, 2024
1331 GMT — Qatar ta ce tana fatan yarjejeniyar tsagaita wuta ta Isra'ila da Hezbollah za ta haifar da tsagaita wuta a Gaza, yayin da sauran kasashen yankin Gulf kamar Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa su ma suka yi maraba da yarjejeniyar.
Qatar, mai shiga tsakani tsakanin Isra'ila da Hamas, ta ce tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hezbollah, za ta iya zama abin koyi ga Gaza, bayan shafe watanni ana tattaunawa ba tare da cim ma wata manufa ba, domin kawo karshen yakin da ake gwabzawa.
Ma'aikatar harkokin wajen Qatar a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce, kasar Qatar ta yi maraba da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cim ma a kasar Lebanon, tana kuma fatan za ta zama abin koyi ga yarjejeniyar makamanciyar wannan domin kawo karshen yakin da ake yi a Gaza.
Ma'aikatar ta ce "Katar ta yi imanin cewa, wannan yarjejeniya za ta ba da damar cim ma matsaya mafi girma da za ta tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin."
1112 GMT — Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 44,282 a Gaza a yayin da take ci gaba da luguden wuta
Isra'ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla 44,282 a Gaza sannan ta jikkata mutum sama da 104,880 tun da ta ƙaddamar da hare-hare a yankin ranar 7 ga watan Oktoban 2023, a cewar Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta Falasɗinu.
"Dakarun Isra'ila sun kashe mutum 33 tare da jikkata mutum 134 a hare-haren kisan kiyashi uku da suka kai wa wasu iyalai a cikin awa 24 da suka gabata," in ji sanarwar da ma'aikatar ta fitar.
0628 GMT — Hamas ta ce a shirye take ta yi tattaunawar tsagaita wuta da musayar fursunoni
Hamas ta ce a shirye take ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, kamar yadda wani babban jami'i na ƙungiyar ta Falasɗinu ya bayyana, inda ya yaba game da tsagaita wuta a Lebanon.
"Mun shaida wa masu shiga tsakani na Masar, Qatar da Turkiyya cewa a shirye Hamas take ta ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma tattaunawa ta gaske game da musayar fursunoni," in ji jami'in, a hira da kamfanin dillancin labarai na AFP, ko da yake ya zargi Isra'ila da yin ƙafar-ungulu kan lamarin.
Ƙarin labarai👇
0551 GMT — Rundunar sojojin Lebanon: 'Muna ɗaukar matakai' na tura sojoji kudanci
Rundunar sojin Lebanon ta ce tana "ɗaukar matakan da suka dace" domin tura dakarunta zuwa kudancin ƙasar awanni kaɗan bayan yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hezbollah ta soma aiki, inda ta gargaɗi mutanen da hare-haren Isra'ila suka kora daga gidajensu da kada su koma har sai ta yanje daga yankin.
"Yanzu tun da yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki, rundunar soji tana ɗaukar matakan da suka kamata domin tura dakarunta zuwa kudanci," a cewar wata sanarwa daga rundunar.
"Rundunar soji tana kira ga mutane da su jira ta kafin su koma gidajensu da ke yankunan fagen-daga waɗanda dakarun maƙiyanmu na Isra'ila suka kutsa ciki, har sai sun janye."