Qatar ta gayyaci jakadan Sweden da ke kasarta don ba shi gargadi kan wulakanta Aklkur'ani da ake yi a babban birnin kasarsa Stockholm, kamar yadda Ministan Harkokin Wajen kasar ya fada.
A wata sanarwa a ranar Juma'a, Ma'aikatar Harkokin wajen Qatar ta ce za ta bukaci hukumomin Sweden su dauki dukkan matakan da suka kamata don dakatar da "dukkan wadannan abubuwan wulakanci da ake yi."
Ita ma Saudiyya ta kira jakadan Sweden a kasarta wanda ke Riyadh in da ta mika masa sakon nuna fushinta kan wulakanta Alkur'anin, kamar yadda Ma'aikatar Harkokin Wajen Saudiyyan ta fada a wata sanarwa.
Riyadh ta yi Allah-wadai "da abin da hukumomin Sweden ci gaba da yi na rashin hankali" wanda yake yawan bai wa masu tsattsauran ra'ayi damar kona tare da wulakanta Alkur'ani Mai Tsarki.
Sannan gwamnatin Saudiyyan ta yi tur da wani shirin kona Kur'ani a Stockholm, a cewar sanarwar.
Hakan na zuwan ne bayan da masu zanga-zanga a Iraki suka cinna wa ofishin jakadancin Sweden wuta a birnin Baghdad tare da ba da umarnin cire jakadan Sweden daga Irakin da kuma janye dukkan wasu harkokin Sweden a kasar, bayan da wani mai tsattsauran ra'ayi ya kona Kur'ani a birnin Stockholm.
"Mun yi tur da babbar murya da wannan mummunan hari a kan littafinmu mai tsarki na Kur'ani, a gaban ofishin jakadancin Iraki a Stockholm a yau," kamar yadda ita ma sanarwar Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta bayyana.
Kazalika Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran ma ta gayyaci jakadan Sweden da ke Tehran "don nuna fushinta sosai a kan wulakanta Kur'ani," kamar yadda kafar yada labaran kasar ta bayyana.
Sanarwar ta Iraki na zuwa ne kwana biyu bayan da wasu masu tsaurin ra'ayi biyu suka zauna a wani waje mai nisan mita 100 daga ofishin jakadancin Irakin a Stockholm.
Daya daga cikinsu wanda kafar yada labaran Sweden ta bayyana da Salwan Momika, wani Kirista dan Iraki mai tsauttsauran ra'ayi da ke zaune a Sweden, ya tattaka tare da yin jifa da Kur'ani, amma bai kai ga kona shi ba.
Sannan kuma sai Momika ya tattaka tutar kasar Iraki.
A ranar 28 ga watan Yuni wato ranar Babbar Sallah ne Momika ya kona Kur'ani a karkashin kariyar 'yan sanda a gaban wani masallaci a Stockholm.
Ita ma Iraki ta "sanar da gwamnatin Sweden... cewa idan har aka sake kona Kur'ani a cikin Sweden to dole ta dauki matakin yanke alakar diflomasiyya."
A hannu guda kuma, shugaban kungiyar Hezbollah ta Labanon, Hassan Nasrallah, ya yi kira ga kasashen Larabawa da na Musulmai da su bi sawun Iraki wajen korar jakadun Sweden daga kasashensu tare da janye nasu jakadun daga Sweden kan wani shirin kona Kur'ani da ake yi a birnin Stockholm.
Nasrallah ya kuma yi kira ga Musulmai da su yi tururuwar halartar Sallar Juma'a su zauna a gaban masallatai "suna rungume da Kur'ani."
Sweden na tsaka mai wuya
Sweden ta fuskanci martani masu tsauri daga kasashen Musulmai kan kona Kur'anin.
A ranar Alhamis, daruruwan 'yan Iraki sun dirar wa ofishin jakadancin Sweden a Baghdad in da suka cinna wuta a zanga-zangar adawa da wani shirin kona Kur'ani da ake tsammanin yi.
Kafin sannan, kasashen duniya da dama da suka hada da Turkiyya da Jordan da Falasdinu da Saudiyya da Moroko da Iraki da Iran da Pakistan da Senegal da Mauritania duk sun yi tur da kuma nuna fushinsu kan kona Kur'anin da aka yi a watan jiya, wani lamari da aka yi bisa izinin hukumomin Sweden.
Dubban mutane a Pakistan da Iraki sun yi zanga-zanga, yayin da Moroko ta yi wa jakadanta kiranye daga Sweden, Iran kuma ta jinkirta aika sabon jakada zuwa Sweden, sannan sauran kasashe suka yi tur da Allah-wadai da abin da ke faruwa a Stockholm.