Babban faretin sojoji a Dandalin Moscow inda sojoji suke baje-kolin kansu da manyan kayan yaki ciki harda garkuwar makamai masu linzami. / Hoto: AP

Shugaban kasra Rasha Vladimir Putin ya shirya gabatar da jawabi a Wajen Taron Ranar Kasa a Moscow, taron da yake sa ran zai gabatar da kishin kasa a yayin da dakarunsa ke ƙara kunna kai Ukraine.

Taron ranar 9 ga Mayu na tuna wa da Nasarar Tarayyar Soviet kan Nazi a Jamus a lokacin yakin duniya na II, kuma daya daga ranakun hutu masu muhimmanci ga Rasha ne a karkashin shugabancin Putin.

Shugaban Rasha ya sha maimaita cewa yakin da suke yi da Ukraine ya zama wajibi kuma suna yakar tsarin Nazi ne.

Ana gudanar da Babban fareti a Jan Dandali, ana gabatar da kayan yaki na Rasha ciki har da garkuwar makamai masu linzami, tare da dubunnan sojoji da suka yi ado a kayan sarki.

Ana yawan gayyatar baki daga kasashen waje zuwa taron.

Shugabanni takwas na kasashen duniya ne za su halarci taron na ranar Alhamis, kamar yadda tashar talabijin ta Rasha ta sanar.

Su ne shugabannin kasashen Belarus, Kazakhstan, Kyrgyzstan, Tajikistan da Turkmenistan - da kuma na Cuba, Laos da Buinea-Bissau,

Fadar Cremlin ta gudanar da taron shugabannin kasashe mambobin kungiyar 'Eurasian Economic Union' - kwana daya kafin faretin.

Putin zai gabatar da jawabin bana a lokacin da dakarunsa ke kara kunna kai Ukraine, da kuma fara sabon wa'adin shekaru shida a kan mulki bayan lashe zabe a watan Maris.

A shekarar da ta gabata sojojin Rasha sun tsaurara hare-hare kan Rasha, kuma suna samun nasara inda Ukraine ke fama da karancin makamai da mayaka.

'Nasara' ga jama'ar Rasha

Mahukunta a Moscow sun tsaurara matakan tsaro a yayin da za a gudanar da faretin na bana, wanda ke zuwa a yayin da ake samun hare-haren jirage marasa matuka daga Ukraine kan iyakokin Rasha.

An gudanar da gwajin faretin tun kwana guda kafin Ranar Nasara.

Sakamakon dalilan tsaro, sauran bangarorin Rasha irin su Yammacin Kursk da Pskov sun dakatar da nasu faretin.

Bikin na zuwa kwanaki biyu bayan Putin ya yi alkawarin kawo wa Rasha 'nasara'.

TRT World