Ministan tsaron Isra'ila ya shaida wa dakarun ƙasar cewa su shirya shiga Gaza, duk da cewa dai bai faɗi yaushe za a fara kutsawar ba.
A wata ganawa da ya yi da sojojin Isra'ilan a kan iyakar Gaza a ranar Alhamis, Yoav Gallant ya buƙaci dakarun da "su kasance cikin shiri" don jiran umarnin shiga ciki.
Duk wanda a da yake hango Gaza daga nesa a yanzu zai ga yadda cikinta yake," ya ce. "Na yi muku alkawari."
Jim kaɗan bayan kalaman Gallant, sai Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya fitar da wani bidiyo nasa da wasu dakaru a kusa da kan iyakar yana yi musu alkawarin samun nasara.
Gaza na cikin ƙawanya
Rikicin da ake yi na yanzu a Gaza, ya fara ne tun ranar 7 ga watan Oktoba da Isra'ila ta fara kai mata hare-hare da sanya mata takunkumai, bayan da Hamas ta ƙaddamar da wasu hare-hare na Operation Al Aqsa Flood, ta ƙasa da ta sama da ta ruwa da ta kai cikin Isra'ilan.
Hamas ta ce ta kai hare-haren ne saboda yawan far wa Masallacin Ƙudus da ake yi da kuma harin da Yahudawa ƴan kama wuri zauna ke kai wa Falasɗinawa.
Daga nan sai Isra'ila ma ta ƙaddamar da kai hare-haren da ta yi laƙabi da Operation Swords of Iron a kan Hamas a cikin Gaza.
Wannan hari na Isra'ila a kan Gaza na daga cikin mafiya muni a cikin shekara 75 ɗin da aka kwashe ana rikici tsakanin ƙasashen, inda Isra'ilan ta sha alwashin ganin bayan Hamas, da sanya Gaza mai yawan al'umma miliyan 2.3 a cikin ƙawanya da kuma kai hare-hare ba ƙaƙƙautawa waɗanda suka kashe dubban mutane tare da raba miliyoyi da muhallansu.
Aƙalla Falasɗinawa 3,785 aka kashe a hare-haren Isra'ila a Gaza, yayin da Isra'ilawa 1,400 kuma suka mutu.