"Abin da Iran ke yi yana da haɗari. Ba lallai sai ka yi amfani da ƙarfin makaman ƙare dangi don gwada sa'arka ba," in ji wani masani. / Photo: Reuters

Hare-haren makamai masu da na jirage marasa matuka da ake kai wa a lokaci guda a kasashen Iraki da Pakistan da Syria ya sanya ayar tambaya kan dalilan da Iran ke da shi na kokarin fadada fadan soji a daidai lokacin da abokan huldarta ke yaƙi da Amurka da Isra'ila.

A cikin 'yan kwanakin da suka gabata Iran ta kai hari kan wani sansani da ake zargin 'yan ta'adda ne a kudancin lardin Balochistan na Pakistan tare da tarwatsa wani gida da makami mai linzami a yankin Erbil na Iraki, wanda Tehran ke zargin jami'an leƙen asirin Isra'ila ne suka yi amfani da su.

An kai hari makamancin wannan a kan 'yan ta'addar Daesh a kasar Siriya, inda mayakan da ke samun goyon bayan Iran suka shafe shekaru suna kai hare-hare.

An samu asarar rayuka a Iraƙi da Pakistan, inda hukumomi a ƙasashen biyu suka ce an kashe fararen hula da suka haɗa da yara a hare-haren na Iran.

Da sanyin safiyar Alhamis Pakistan ta mayar da martani da matakin da ya dace a lardin Balochestan-Sistan na Iran a wani abin da Islamabad ta ce maɓoyar wata kungiyar 'yan aware ta Baloch ce.

"Da alama rikicin siyasar cikin gida na Iran ne yake jawo irin waɗannan hare-haren. Akwai buƙatar su mayar da martani a kan harin ƙunar baƙin wake da aka kai hubbaren Suleimani wanda ya kashe mutane da dama," a cewar Ryan Bohl, wani babban manazarci a yankin Gabas ta Tsakiya a cibiyar tuntuba ta RANE Network kan hadarin leken asiri, a hirarsa da TRT.

"Don haka suna buƙatar su nuna ƙarfi da cewa suna da ikon yin maganin waɗanda suka aikata akan."

Bohl yana magana ne kan harin da aka kai a ranar 3 ga watan Janairu a kusa da kabarin Janar Qasem Soleimani da ke birnin Kerman na kasar Iran, inda sama da mutum 100 suka mutu.

Kungiyar Daesh ce ta dauki alhakin kai harin, kuma masu sharhi na ganin cewa akwai yiwuwar reshen kungiyar ta'addancin da ke Afganistan ne suka kai shi. Tashin bama-baman dai ya fallasa irin kura-kuran da ke tattare da jami'an tsaron kasar Iran, lamarin da ya sanya matsin lamba ga gwamnatin Shugaba Ebrahim Raisi da ta dauki mataki.

Bohl ya ce martanin da Iran ta mayar, musamman harin da aka kai kan kungiyar da ake zargin ta 'yan ta'addan Jaish al Adl ce da ke Pakistan, wani yunƙuri ne na zagon ƙasa, domin a maimakon haka ya kamata Tehran ta kai hari kan 'yan ta'addar Daesh a cikin Afghanistan.

"Ba sa so su ƙara ta'azzara halin da ake ciki da 'yan Taliban a halin yanzu. Sun riga sun sa dangantaka tsakanin su ta yi tsami sakamakon fadan kan iyaka da suke ta yi.

"Da alama suna kokarin nemo wani ne da za su iya a yankin, ta hanyar kafafen yada labarai na kasar, don su nuna tamkar Daesh ne, don dacewa da manufofinsu na cikin gida."

Fargabar ƙara samun yaƙi a Gabas ta Tsakiya

Amurka da ƙawayenta suna kai wa 'yan tawayen Houthi na kasar Yemen da ke da alaƙa ta ƙut da ƙut da Iran hari, saboda kawo cikas ga kasuwancin duniya a Tekun Maliya. Houthi sun ce hare-haren makamai masu linzami da kuma yunkurin sace jiragen ruwan dakon kaya martani ne ga yakin da Isra'ila ke yi a Gaza.

Akwai fargabar cewa arangamar Amurka da Houthi na iya haifar da wani yaki a yankin da ke fama da rikici.

"Muna ganin Iran ta shiga yanayi na rashin zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya saboda daukar nauyin 'yan ta'adda," in ji Michael Kugelman, Daraktan Cibiyar Kudancin Asiya a Cibiyar Wilson.

"Tana fargabar cewa sha'awarta ta tsaro za ta ƙaru sosai. Don haka ina ganin tana kokarin kai hare-hare tare da kai farmaki kan wurare daban-daban masu adawa da Iran. Kuma hakan ya hada da Pakistan a wannan lamarin."

Mummunan martanin da Pakistan ta mayar, wanda ya biyo bayan matakin Islamabad na kiran jakadanta a Tehran, na iya ƙara ruruta wutar rikicin da ke tsakanin maƙwabtan, wadanda ke da iyaka da juna.

Bangarorin biyu dai sun nuna wa juna yatsa bisa zargin suna da alaka da kungiyoyin da ke adawa da kasar. Pakistan na zargin Iran da karbar bakuncin 'yan awaren da ke da hannu a rikicin da aka kwashe shekaru ana yi a lardin Balochistan. Iran ta ce Pakistan na karbar bakuncin kungiyoyin 'yan ta'adda.

"Abin da Iran ke yi yana da haɗari. Ba lallai sai ka yi amfani da ƙarfin makaman ƙare dangi don gwada sa'arka ba," in ji Kugelman.

A lokaci guda kuma, Pakistan na fafutukar magance matsalar da tattalin arzikinta ke fuskanta, da sabbin hare-hare daga ƙungiyar Tehreek-e-Taliban Pakistan da kuma faɗan cikin gida gabanin zaɓukan da za a yi a ƙasar ranar 8 ga watan Fabrairu.

"Ba za ta iya jurewa shiga wani sabon rikici da maƙwabtanta ba," in ji Kugelman.

Kazalika akwai miliyoyin Musulmai mabiya Shi'a a Pakistan - wadanda yawansu ya kai kashi 15 zuwa 20 cikin 100 na al'ummar ƙasar.

Harbin gargaɗi

Harin makami mai linzami da Iran ta harba a yankin Kurdawa da ke arewacin Iraƙi ya sanya manazarta nuna shakku kan hakikanin manufar Tehran. Iran ta ce ta kai hari kan wata cibiyar leken asiri ta Isra'ila, wadda ke aiki a kusa da karamin ofishin jakadancin Amurka da ke Erbil.

Mayakan da ke samun goyon bayan Iran suna da karfi sosai a Iraki, inda suka kwashe shekaru da dama suna kai hare-hare kan sojojin Amurka.

"Za su iya mayar da martani ta hanyar aikewa da mayakansu. Amma zabin amfani da makamai masu linzami masu cin dogon zango shi ne kuma manufar aika sako ga Amurkawa da Isra'ilawa," in ji Bohl na cibiyar sadarwa ta RANE.

"Suna cewa idan aka samu ta'azzara a wasu wurare, karfin makamansu na makami mai linzami ya ci gaba da kasancewa a wurin kuma kamar yadda suke a shekarun baya."

TRT World