Hoton duniyar wata, wanda na'urar Chandrayaan-3  ta dauko. Hoto Reuters

Ga abun da aka sani game da wanzuwar daskararren ruwa a duniyar wata - da kuma me ya sa hukumomin bincike kan sararin samaniya da kamfanoni masu zaman kansu suke kallon wajen a matsayin cibiyar duniyar wata, gano Duniyar Wata da share fagen zuwa Duniyar Mars.

Ta yaya masana kimiyya suka gano ruwa a duniyar wata?

A tun farkon 1960, kafin kumbon Apollo na farko ya sauka, masana kimiyya sun yi hasashen cewa akwai yiwuwar a samu ruwa a duniyar wata.

Samfurin da 'yan sama jannati da ke cikin Apollo suka dawo da shi a karshen 1960 da farkon 1970 ya bayyana wajen a bushe yake.

A 2008, masu bincike a Jami'ar Brown sun sake nazari kan samfurin da aka dauko daga duniyar wata da sabuwar hanyar fasaha inda suka gano iskar hydrogen a cikin wasu kura-kuran duwatsu.

A 2009, wani kumbon NASA dauke da masu bincike kuma 'yan sama jannati na Hukumar Bincike Kan Sararin Samaniya ta Indiya Chandrayaan-1 sun gano akwai ruwa a Duniyar Wata.

A wannan shekarar dai, NASA ta tabbatar da gano daskararren ruwa a iyakar Kudancin Dduniyar Wata.

Aikin NASA na farko, shirin zuwa duniyar wata a 1998, ya gano alamun cewa bangaren kudancin duniyar wata ne ke da daskararren ruwa a kwance.

Me ya sa samuwar ruwa a duniyar wata yake da muhimmanci?

Masana kimiyya suna mayar da hankali wajen wuraren da ake samun dadadden ruwan kankara saboda za su iya gano bayanan aman wutar duwatsu, da abubuwan da taurari masu wutsiyya da duwatsun da ke yawo a sararin samaniya ke jehowa duniya, da kuma asalin tekuna.

Idan har akwai isasshen ruwan kankara a duniyar wata, zai zama ruwan sha ga masu zuwa duniyar, kuma zai taimaka wajen sanyaya na'urori.

Sannan za a iya amfani da ruwan wajen samar da iskar hydrogen ga mai da ma iskar oxygen ta shaka, wanda hakan zai kuma share fagen zuwa Duniyar Mars.

A 1967, Yarjejeniyar Zuwa Duniyar Wata ta Majalisar Dinkin Duniya ta haramta wa kowacce kasa bayyana mallakar Duniyar Wata. Babu wani tanadi da ya hana ayyukan kasuwanci.

Wani kokari da Amurka ke jagoranta ya samar da wasu ka'idojin zuwa duniyar wata, da kuma amfani da kayayyakinsu. Yarjejeniyar Artemis ta samu sanya hannun mutum 27. China da Rasha ba su saka hannu ba.

Me ya sa iyakar Kudancin Duniyar Wata ke jan hankali?

Kokarin sauka a Duniyar Wata bai samu nasara ba da farko. An shirya kumbon Luna-25 na Rasha zai sauka a Duniyar Wata a wannan makon, amma sai ya kauce daga kan hanya tare da tarwatsewa a ranar Lahadi.

Bangaren Kudancin Duniyar Wata - nesa daga yankin equator ne wajen da a baya aka yi ta kokarin zuwa, hakan ya hada da saukar kumbon Apollo da yawa.

Shirin Chandrayaan-3 na ISRO na ci gaba don sauka a ranar Laraba, in ji hukumar sararin samaniyar.

A 2019 shirin Indiya bai yi nasara ba wajen sauka a kusa da wajen da Chandrayaan-3 zai je.

Amurka da China sun shirya zuwa Kudancin Duniyar Wata.

Reuters