Bayan faduwar rokar, Moscow ta fara gudanar da bincike kan dalilan da suka haddasa hadarin rokarta samfurin Luna-25. Hoto: Reuters

Jirgin sama jannatin Rasha samfurin 'Luna-25' da aka aika Duniyar Wata ya bar wani wagegen rami mai fadin mita 10 a Duniyar Watan bayan hatsarin da ya yi a watan jiya sakamakon wata matsala da ta rutsa da shi.

Jirgin ya samu matsala ce yayin da yake kokarin sauka a Kudancin Duniyar Wata, a cewar hotunan da Hukumar kula da sararin samaniyar Amurka NASA ta fitar.

Jirgin shi ne na farko cikin shekara 47 da Rasha ta aika Duniyar Wata, inda a ranar 19 ga watan Agusta ya yi hatsari bayan wata matsala da jirgin ya samu da ta kai ga fadawa cikin Wata, lamarin da ya nuna koma bayan da Tarayyar Soviet ta samu a gagarumin shirinta na zuwa sararin samaniya.

Wata nau'rar daukar hoto ta sararin samaniya ta hukumar binciken sararin samaniya ta Amurka LRO ta yi hoton wani wakeken rami a kan wata wanda aka tabbatar da cewa tasirin hatsarin jirgin Luna 25 na kasar Rasha ne ya haifar.

"Girman ramin ya kai kimanin mita 10 a ma'unin diyamita,"a cewar NASA.

"Tun da aka gano sabon ramin kusa da inda rokar ta fado, tawagar LRO ta ce mai yiwuwa tasirin hatsarin jirgin ne ya jawo hakan."

Fara bincike

Bayan faduwar jirgin, Moscow ta ce an kafa wani kwamiti na musamman da zai binciki dalilan da suka haddasa hatsarin rokar samfurin Luna-25.

Duk da cewa an yi ta gwada tafiya zuwa Duniyar Wata, hatsarin da rokar Rasha ta yi ya nuna rashin karfin da kasar ke da shi wajen zuwa sararin samaniyar a yanzu, tun bayan nasarar da ta samu a zamanin da aka yi gasar yakin cacar baka da Moscow ta kasance ta farko da ta harba tauraron dan adam da ya kewaya duniya - 'Sputnik 1' a shekarar 1957.

Sai kuma mutum na farko dan Soviet Yuri Gagarin da ya fara zuwa sararin samaniya a shekarar 1961.

TRT World