Kwanaki kadan bayan da jirgin sama jannatin Indiya ya sauka a Kudancin Duniyar Wata, hukumar sararin samaniyar kasar ta ce za ta kaddamar da tauraron dan'adam da zai yi bincike a Duniyar Rana.
"Za a kaddamar da rokar Aditya-L1, jirgin sama jannati na farko na Indiya da zai yi bincike a kan Rana, ranar 2 ga watan Satumba," a cewar sanarwar da Hukumar Binciken Samaniya ta Indiya (ISRO) ta fitar a ranar Litinin a shafin X.
Za a harba kumbon Aditya, da ke nufin "rana" da Indiyanci, zuwa wani bigiren zagayen haske a wani yanki na sararin samaniya mai nisan kilomita miliyan 1.5 daga Duniyar Earth, inda jirgin zai dinga hango abin da ke sararin ranar sosai.
"Hakan zai samar da wata babbar dama ta fahimtar al'amuran da ke faruwa a sararin Duniyar Rana da tasirinsu a kan yanayin sararin samaniya da lokaci," in ji ISRO.
Jirgin sama jannatin zai dauki kayayyakin aiki bakwai don nazarin sararin Duniyar Ranar - wadanda ake kira da photosphere da chromosphere — da suka hada da amfani wasu na'urorin gano karfin lantarki da zafin wajen.
Daga cikin abubuwa da yawa da za a duba har da wadanda ke bayar da yanayi a sararin samaniya.
A yayin da hukumar sararin samaniya ta Amurka NASA da ta Turai ESA suka sha aika na'urori don nazarin Rana, ita kuwa Indiya wannan ne karo na farko da za ta yi irin wannan hobbasa.
Injiniyoyi masu fasaha
A makon da ya wuce ne jirgin sama jannatin Indiya da bai dauki kowa ba mai suna Chandrayaan-3 ya sauka a Duniyar Wata, inda hakan ya sa Indiya ta zama kasa ta hudu baya ga Amurka da Rasha da China da ta yi nasarar zuwa Duniyar Watan.
Hakan ya zamo gagarumar nasara ta baya-bayan nan da Indiya ta samu a burinta na zuwa sararin samaniya, lamarin da ya jawo murna a fadin kasar wacce ta fi kowacce yawan al'umma a duniya.
Kasafin kudin Indiya na shirin zuwa sararin samaniya ba shi da yawa idan aka kwatanta da sauran manyan kasashen duniya, amma tana ci gaba da kokarin bincike a Duniyar Wata tun shekarar 2008.
Kwararru sun ce Indiya za ta iya ci gaba da bincikenta ba tare da kashe makudan kudade ba ta hanyar amfani da fasahar da aka taba amfani da ita a baya, sannan kuma godiya ga kwararrun injiniyoyinta wadanda albashinsu bai ko kama kafar na takwarorinsu da ke kasashen waje ba.
A shekarar 2014, Indiya ta zama kasar yankin Asiya ta farko da ta aika jirgin sama jannati ya yi zagaye a Duniyar Mars, sannan ta saka ranar da za ta kaddamar da zagaye a sararin Duniyar Earth na tsawon kwana uku a badi.
Ta kuma shirya wani shirin hadin gwiwa da Japan don sake kaddamar da wani binciken a Duniyar Wata nan da shekarar 2025, da kuma shirin bincike a Duniyar Venus nan da shekara biyu.