1730 GMT — Me jirgin yaƙin Amurka yake yi a Isra’ila? — Shugaba Erdogan
Shugaban Turkiyya Recep Tayyib Erdogan ya yi wasu jawabai kan yaƙin Isra'ila da Gaza a yayin da yake jawabi ga wazirin kasar Wazirin Austria, Karl Nehammer da ya karɓi baƙuncinsa a Ankara.
Shugaba Erdogan ya ce:
- - Me jirgin yaƙin Amurka yake yi a Isra’ila?
- - Hakan zai aiwatar da mummunan kisan kiyashi ne ta hanyar kai hari da lalata Gaza
- - Sannan kuma Amurka na da fiye da sansanoni 23 a Syria; mene ne ƙudurinsu?
- - Duk da cewa Turkiyya da Amurka mambobin NATO ne, Amurka ta harbo jirgi marar matukinmu a Syria; wane kallo za mu yi wa hakan?
Ya ƙara da cewa:
- - Zan ci gaba da ƙoƙarin diflomasiyya don samun zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya
- - Hakan zai yiwu ne kawai ta hanyar samar da mafita ta dindindin kan rikicin Isra’ila da Falasdinu
- - Mazauna Gaza na fuskantar hare-hare ba ƙaƙaƙautawa daga Isra’ila
- - Za mu ci gaba da yin bakin ƙoƙrinu don dakatar da wannan rikicin nan ba da daɗewa ba.
1645 GMT — An kashe ƴan jaridar Falasɗinu huɗu a harin da Isra'ila ta kai Gaza: Ƙungiyoyin ƴan jarida
An kashe wasu ƴan jarida huɗu na Falasɗinu a hare-haren saman da Isra'ila ta kai Gaza, kamar yadda ƙungiyoyin ƴan jarida da jami'ai suka ce, a yayin da aka shiga kwana na huɗu ana kau hare-hare da yaƙi.
Shugaban ofishin yaɗa labarai na ƙungiyar Hamas da ke Gaza, Salameh Maarouf, ya bayyana mutum uku daga cikin ƴan jaridar a matsayin Said Al Taweel, daraktan kamfanain dillancin labarai na Al Khamisa da ɗan jarida mai ɗaukar hoto Mohammed Sobboh da kuma Hisham Nawajhah, wani wakilin kamfanin dillancin labaran Gaza.
An kashe su ne a wani hari da aka kai a lokacin da suka ɗaukar rahoto kan kwashe mutane da ake yi daga wani rukunin gidaje da ke kusa da gabar tekun da ake kamun kifi na birnin Gaza, a cewar Maarouf, yana yin Allah wadai da "halayyar cin zali" a kan ƴan jarida ta Isra'ila.
1630 GMT — Faransa tana adawa da dakatar da taimakon agaji na EU dungurungum ga Falasdinawa
Faransa ta ƙi amincewa da kiraye-kirayen cewa a dakatar da taimakon agaji ɗungurungum na Ƙungiyar Tarayyar Turai ga Falaɗinawa.
"Ba ma goyon bayan dakatar da agajin da ke amfanar Falasɗinawa kai tsaye," Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya shaida wa manema labarai, bayan wani taro na ministocin ƙasarsa da Jamus da aka yi a Hamburg.
Ya ce tuni an fara nazari don tabbatar da cewa kayayyakin agajin da aka yi niyyar kai wa Falasɗinawa bai tafi ga taimakawa ayyukan ƙungiyar Hamas ba.
"Ana amfani da tallafin ne wajen samar da ruwa da ayyukan lafiya da abinci da ilimi ga fararen hula," ya ce.
Macron ya ce bai kamata matakan yaƙi da ta'addanci su daƙile ƙoƙarin taimakon fararen hular da ba su ji ba ba su gani ba da kuma warware matsalolinsu da biyan buƙatunsu na abubuwan rayuwa.
1540 — Isra'ila ta kashe Falasdinawa 765, in ji Ma'aikatar Lafiya
Ma'aikatar Lafiya ta Falasdinu ta ce kawo yanzu jiragen yakin Isra'ila sun kashe Falasdinawa 765 a rana ta uku ta luguden wutan da suke yi a Gaza.
Ma'aikatar ta ce Falasdinawa akalla 4,000 ne suka jikkata sakamakon hare-haren Isra'ila.
1138 — Isra'ila za ta tattaro sojojinta na ko-ta-kwana 360,000
Gwamnatin Isra’ila a ranar Talata ta bayyana cewa ta amince a tattaro sojojinta na ko-ta-kwana 360,000 a daidai lokacin da take yaki da Falasdinawa a Gaza.
Shafin intanet na Ynet ya ruwaito cewa rundunar sojojin Isra’ila ta tura jirgin yaki domin tattaro sojojin daga Turai su shiga yakin.
A wata sanarwa da aka fitar, sojojin Isra’ila sun bayar da shawara ga Falasdinawa su bar Gaza su gangara kusa da Masar a daidai lokacin da ake ci gaba da fafatawa, da kuma yiwuwar shiga cikin Gaza domin bude wuta.
“Rafah a bude take. Duk wanda zai iya fita ina bayar da shawarar ya fice,” kamar yadda Times of Israel ta ruwaito Richard Hecht yana bayyanawa.
1110 GMT — 'An gano gawarwakin Falasdinawa 'yan bindiga 1,500 a Isra'ila, in ji wani sojin Isra'ila
Wani jami'in sojin Isra'ila ranar Talata ya ce sojojinsu sun gano "gawarwaki 1,500" na Falasdinawa 'yan bindiga a yankun kasar.
"A cikin kwanakin da suka gabata, sojojin Isra'ila sun gano akalla gawarwaki 1,500 na Falasdinawa 'yan bindiga a yankunan Isra'ila," in ji jami'in sojin a hirarsa da kamfanin dillancin labaran Anadolu na kasar Turkiyya, ko da yake ya bukaci a sakaya sunansa.
Sai dai bai yi cikakken bayani kan batun ba.
Amma ya zuwa wannan lokaci kungiyar Hamasa ta Falasdinawa ba ta ce komai a kan wannan ikirari ba.
0940 GMT — Yariman Saudiyya ya jaddada goyon bayan kasar ga Falasdinawa
Yariman Saudiyya Mai Jiran Gado kuma firaiministan kasar, Mohammed bin Salman ya jaddada goyon bayan Saudiyya ga Falasdinawa.
Yariman ya bayyana haka ne ta wayar tarho a lokacin da yake magana da Shugaban Falasdinu Mahmoud Abbas a ranar Litinin.
Shugabannin sun yi tattaunawa mai yawa, inda suka tattauna batun yadda za a shawo kan rikicin da ake fama da shi a Gaza da sauran wurare masu makwaftaka, kamar yadda jaridar Saudi Gazette ta Saudiyya ta ruwaito.
Baya ga Yariman Saudiyya, Shugaban Falasdinu Mahmoud Abbas ya yi magana da shugabannin kasashen Larabawa da dama wadanda suka hada da Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi da Shugaban Jordan Abdullah II.
Haka kuma ya tattauna da Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Al-Thani.
0855GMT — Isra'ila ta kai hari sau 200 a Gaza cikin dare
Sojojin Isra’ila a ranar Talata sun sanar da cewa sun kaddamar da hare-hare ta sama fiye da sau 200 a Gaza a cikin dare, inda suka yi ikirarin kai farmaki kan kayayyakin soji na Falasdinawa.
A wata sanarwa da ta fitar a shafin X, sojojin Isra’ila sun bayyana cewa jiragensu na yaki da na ruwa sun kai hari kan wuraren da Hamas ke ajiyar makamai. Sojojin na Isra’ila sun kuma yi ikirarin cewa Hamas din na boye makamai a cikin Masallaci.
Sojojin sun kuma ce sun kai hari a wani rukunin gidaje wanda ake amfani da shi wurin ajiye makaman da ke harbin motocin igwa.
Sai dai a nasa bangaren, Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida a Gaza ta sanar da cewa duka hare-haren da Isra’ila ta kai, sun fada ne a kan fararen hula da gidajen jama’a.
0805 GMT — Sojojin Isra’ila a ranar Talata sun sanar da cewa an kashe dakarunsu 123 tun bayan da yaki ya barke tsakanin kungiyar Hamas ta Falasdinawa da kuma Isra’ila a karshen makon da ya gabata.
Shafin intanet na kafar watsa labarai ta The Times of Israel ya ruwaito cewa Isra’ila ta saki karin sunayen sojojinta 38 wadanda aka kashe a lokacin da ake yaki a kwanaki uku da suka wuce, wanda hakan ya kawo adadin zuwa 123.
A halin yanzu adadin ‘yan Isra’ila da aka kashe ya kai 900, sannan mutum 2,616 suka samu rauni.
Dangane da ‘yan Isra’ila kuwa wadanda aka yi garkuwa da su a Gaza, zuwa yanzu hukumomin Isra’ila ba su bayyana adadinsu ba.
Duk da cewa sojojin Isra’ila sun sanar da iyalai sama da 100 kan cewa ‘yan uwansu na hannun Hamas, amma jakadan Isra’ila a Majalisar Dinkin Duniya Gilad Erdan ya kiyasta cewa adadin wadanda ake rike da su na tsakanin 100 zuwa 150.