0013 GMT — MDD ta nemi a yi bincike mai zaman kansa kan kisan da Isra'ila ta yi wa Falasɗinawa masu jiran tallafi a Gaza
Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres ya ce akwai buƙatar gudanar da bincike mai zaman kansa sakamakon kisan da Isra'ila ta yi wa Falasɗinawa sama da 100 da ke jira a ba su kayan tallafin jinƙai a Gaza.
Da yake magana a St. Vincent da the Grenadines gabanin taron shugabannin yankin, Guterres ya ce ya yi matuƙar "kaɗuwa" game da kisan da Isra'ila take yi wa waɗannan bayin Allah, inda hukumomin Falasɗinu suka ce kawo yanzu ta kashe fararen-hula fiye da 30,000 daga ranar 7 ga watan Oktoba.
Guterres ya yi raddi game da matakin baya bayan nan na Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya na neman tsagaita wuta, inda ya ce rashin jituwar da ake samu tsakanin ƙasashe ta sa ana "hawa kujerar na-ƙi don daƙile ayyukan" kwamitin.
2327 GMT — Kungiyar EU ta yi Allah wadai da harin da Isra'ila ta kai wanda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa 112
Babban jami'in harkokin wajen Tarayyar Turai Josep Borrell ya yi Allah wadai da kisan da Isra'ila ta yi wa Falasdinawa 112 a lokacin da ake raba kayan agaji a Zirin Gaza da aka yi wa ƙawanya, yana mai cewa kisan sam bai dace ba.
"Na firgita da labarin sake yin wani kisan gilla a kan fararen hula a Gaza waɗanda ke neman agaji," in ji shi a shafin X.
"Ba za a yarda da wannan kisa ba."
Harbe-harben da Isra'ila ta yi, a cewar shaidu da likitoci, sun kuma jikkata Falasdinawa 760 waɗanda ke fama da yunwa.
2300 GMT — Isra'ila sun kashe Falasɗinawa 112 ta hanyar 'harbin su a kai'
Jakadan Falasdinawa a Majalisar Dinkin Duniya ya zargi Isra'ila da kai hari kan ayarin motocin jinƙai "da gangan", yana mai cewa da dama daga cikin Falasɗinawa 112 da suka kashe harbin su aka yi a kai.
Riyad Mansour ya shaida wa manema labarai gabanin rufe taron gaggawa na kwamitin sulhu na MDD cewa a wasu ƴan kwanakin manyan motoci ɗauke da kayayyakin jinƙai irin su fulawa da sukari da sauran kayayyakin masarufi, na zuwa arewacin Gaza don bayar da agaji ga Falasɗinawan da ke tsananin bukatar taimako.
Ya ce manyan motocin sun yi irin wannan aiki a safiyar ranar Alhamis, kuma dubban Falasdinawa na can a lokacin.
"Sai kuma kwatsam sojojin Isra'ila suka fara harbe-harbe a kansu, kuma a cewar bayanan da muka samu, da dama daga cikinsu an harbe su kawunansu," in ji shi.
Mansour ya ce "Ba wai an yi harbin a iska ba ne fa da nufin tarwatsa mutane."
"An kai hari da gangan da nufin kashe su, kuma adadin da muke da shi a yanzu na waɗanda aka kashe ya kai 112, kuma adadin yana ƙruwa, sannan an jikkata wasu mutum 750."
0034 GMT — Macron ya yi kira da a tsagaita wuta cikin gaggawa a Gaza
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi kira da a tsagaita wuta cikin gaggawa a Gaza a yau Juma'a kuma ya ce halin da ake ciki a Gaza ya yi muni.
"Akwai ɓacin rai a kan hotunan da ke fitowa daga Gaza inda sojojin Isra'ila suka kai wa fararen hula hari. Ina matuƙar kakkausar suka ga wadannan harbe-harbe tare da yin kira ga gaskiya, adalci, da mutunta dokokin ƙasa da ƙasa," in ji Macron a wani sakon da ya wallafa a dandalin sada zumunta na X.