Gidan rediyon Isra’ila ya bayyana cewa mayakan Hamas sun yi garkuwa da dakarun Isra’ila 35. Hoto/Reuters

Kungiyar da ke ikirarin Jihadi ta Falasdinawa wato Hamas ta kaddamar da wani harin mafi girma a tsawon shekaru ga Isra’ila a ranar Asabar.

Ma'aikatar lafiya ta Isra'ila ta bayyana cewa akalla mutum 545 aka raunata a harin da Falasdinawan suka kai.

Haka kuma hukumar bayar da agajin gaggawa ta Isra'ila ta ce akalla 'yan Isra'ila 22 aka kashe sakamakon harin.

Rahotanni sun ce mayakan na Hamas sun shammaci dakarun na Isra’ila da safiyar Asabar inda suka kutsa cikin Isra’ila ta ruwa da ta kan tudu tare da bude wuta.

Haka kuma mayakan na Hamas sun kai farmaki wasu sansanonin soji na Isra’ila.

Gidan rediyon Isra’ila ya bayyana cewa mayakan Hamas sun yi garkuwa da dakarun Isra’ila 35.

Wani mai magana da yawun sojojin Isra'ila ya bayyana cewa Falasdinawa sun harba makaman roka akalla 2,500 cikin Isra'ila, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

Shugaban sojin Hamas, Mohammed Deif ya sanar da cewa sun soma wani shiri mai suna “Operation Al-Aqsa Storm.”

“A yau mutane suna sake samun juyin-juya halinsu,” kamar yadda ya bayyana a wani sakon murya a lokacin da ya yi kira ga Falasdinawa daga gabashin Birnin Kudus zuwa arewacin Isra’ila kan su shiga yaki domin yakar “wadanda suka mamaye su da kuma rusa bango.”

Wannan harin na zuwa ne bayan an kashe wani Bafalasdine a lokacin wata arangama tsakanin wasu mazauna Isra’ila ba bisa ka’ida ba a birnin Huwara da ke Gabar Yamma da Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye inda har aka yi sabon rikici a lokacin jana’izarsa har mutum tara suka jikkata.

An shafe shekaru ana rikici tsakanin dakarun Isra'ila da mayakan Hamas. Hoto/Reuters

Harba makaman roka

An harba makaman roka daga wasu sassa na yankunan da Falasdinawa suke tun daga 06:30 na safe, wato 03:30 kenan agogon GMT, inda aka ci gaba da harba makaman har tsawon minti talatin, kamar yadda wani dan jarida na kamfanin dillancin labarai na AFP ya bayyana.

Sojojin Isra’ila sun kunna jiniya ta gargadi a fadin kudancin kasar, inda ‘yan sanda suka gargadi jama’a da su tsaya kusa da wuraren da ake bayar da kariya daga hare-haren bama-bamai.

An ta jin karar hare-hare a kusa da birnin Tel Aviv da kuma wajen Birnin Kudus da aka mamaye.

Isra’ila ta zagaye tare da hana shige da fice ba da izini ba cikin Gaza tun daga shekarar 2007.

Tun daga lokacin mayakan Falasdinu da kuma sojojin Isra’ila suke fafata yaki.

Takunkumin da aka saka wa Gaza, ya hana mutane da kayayyaki shiga da fita wanda hakan ya jawo koma baya ga tattalin arzikinsu.

Reuters
AFP