Pezeshkian, mai shekara 69, wanda likitan fiɗa ne kuma ɗan siyasa mai ra'ayin sauyi, ya yi nasara da ƙuri'u miliyan 16.3 yayin da Jalili ya samu ƙuri'u miliyan 13.5 a zaɓen da aka gudanar ranar Juma'a.  / Hoto: Reuters

Masoud Pezeshkian, likitan zuciya kuma ɗan siyasa mai ra'ayin sauyi, wanda kuma ɗan majalisar dokoki ne da ya yi alƙawarin tattaunawa da ƙasashen Yamma, ya lashe zaɓen Iran zagaye na biyu, bayan ya kayar da Saeed Jalili, a cewar gidan talbijin na ƙasar kamar yadda Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta tabbatar.

Sakamakon da aka fitar ranar Asabar da safe ya nuna cewa Pezeshkian ya yi nasara da ƙuri'u miliyan 16.3 yayin da Jalili ya samu ƙuri'u miliyan 13.5 a zaɓen da aka gudanar ranar Juma'a.

'Yan ƙasar Iran sama da miliyan 61 ne suka cancanci kaɗa ƙuri'a, kuma daga cikinsu mutum miliyan 18 suna tsakanin shekaru 18 zuwa 30. An bayyana cewa za a rufe rumfunan zaɓe da misalin ƙarfe 6 na yamma sai dai an tsawaita lokacin kaɗa ƙuri'a zuwa tsakar dare domin bai wa ƙarin mutane damar jefa ƙuri'unsu.

Pezeshkian da Jalili sun fafata a zaɓen ne domin maye gurbin tsohon shugaban Iran Ebrahim Raisi, mai shekaru 63, wanda ya mutu a watan Mayu sakamakon hatsarin jirgin helikwafta, wanda kuma ya yi sanadin mutuwar Ministan Harkokin Cikin Gida da wasu manyan jami'an gwamnati.

Pezeshkian bai yi alƙawarin kawo gagarumin sauyi a tsarin gudanar da mulkin Iran ba sannan ya ce Shugaban Addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei ne mai wuƙa da nama kan dukkan harkokin ƙasar.

Lokacin yin kaffa-kaffa

Mgoya bayan Pezeshkian sun ɓarke da murna a kan titunan Tehran da sauran manyan biranen Iran kafin asubahi a yayin da tazarar da ke tsakaninsa da take ci gaba da faɗaɗa Jalili.

Sai dai nasarar Pezeshkian ta samu ne a lokacin da ya kamata a yi kaffa-kaffa sakamakon rikicin da Gabas ta Tsakiya ke ciki game da yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza.

Dukkan 'yan takarar sun yi ta fama wajen karkato da ra'ayin 'yan ƙasar kan su jefa ƙuri'unsu a zaɓen da ba a fito sosai ba.

Jami'an gwamnati da ke da kusanci da Shugaban Addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei sun yi hasashen fitowar masu kaɗa ƙuri'a sosai a yayin da ake tsaka da zaɓen, sannan gidan talbijin na ƙasar ya riƙa nuna hotunan masu kaɗa ƙuri'a a layukan zaɓe a faɗin ƙasar.

An gudanar da zaɓen shugaban Iran ne a yayin da yankin yake tsaka da yaƙi. A watan Afrilu, Iran ta ƙaddamar da hare-hare a karon farko da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa kai-tsaye zuwa Isra'ila kan yaƙin da take yi a Gaza.

TRT World