A 2017, Raisi ya yi takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin PFIR  masu ra'ayin riƙau inda ya ƙalubalanci Hasan Rouhani da ke mulki a lokacin kuma mai ra'ayin kawo sauyi a Iran. .  OTHERS / Photo: Reuters

Mahukunta a Iran sun tabbatar da mutuwar shugaban ƙasar Ebrahim Raisi da Ministan Harkokin Waje Amirabdollahian a hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a yammacin Iran a ranar Lahadi 19 ga Mayu, 2024.

Jirgin na ya faɗo ne a wani yanki da ke kusa da iyakar Azerbaijan da Iran, a yayin da ake fuskantar rashin kyawun yanayi da ƙarancin gani, kamar yadda Tehran da kafar yaɗa labaran gwamnati suka sanar.

Awanni kafin hatsarin jirgin mai saukar ungulu kirar Amurka, Raisi ya ziyarci Azerbaijan don ƙaddamar da aikin madatsar ruwa ta haɗin gwiwa a tafkin Aras, wanda ke nuni ga ingantuwar alaƙarsu da ƙasashe maƙota.

Kafafan yaɗa labarai na gwamnatin Iran sun bayyana cewa shugaba Raisi ya samu rakiyar Ministan Harkokin Ƙasashen Waje Amirabdollahian, da gwamnan yankin Azerbaijan ta Gabas a Iran da sauran jami’ai da masu kare lafiyar shugaban ƙasa.

Bayan kwashe tsawon awanni suna fama, masu aikin ceto tare da taimakon jiragen sama da tauraron ɗan'adam, sun gano gawarwaki da tarkacen jirgin mai saukar ungulu a yankin da hatsarin ya afku.

Wane ne Raisi?

An san shugaban ƙasar na Iran mai shekara 64 da ra'ayin riƙau, kuma ya ƙalubalanci masu matsakaicin ra'ayi da masu son kawo sauyi a matsayinsa na ɗan takarar masu ra'ayin riƙau a zaɓukan da suka gabata.

A 2017, Raisi ya yi takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin PFIR masu ra'ayin riƙau inda ya ƙalubalanci Hasan Rouhani da ke mulki a lokacin kuma mai ra'ayin kawo sauyi a Iran

A yayin da ya sha kaye a hannun Rouhani a zaɓen 2017, ya lashe zaɓen shugaban ƙasar a 2021 bayan da Majalisar Shura, Hukumar da ke tantance masu tsayawa takara, ta soke takarar masu rajin kawo sauyi da masu matsakaicin ra'ayi 32 kafin gudanar da zaɓen.

Manazarta da dama sun kalli matakin majalisar a matsayin share wa Raisi hanyar zama shugaban ƙasa. Raisi wanda a baya ya rike manyan muƙamai ciki har da Alƙalin Alƙalan Iran, shugaban Hukumar Shari'a, ya kuma kasance makusanci ga shugaban Addini na Iran Ali Khamenei.

Kazalika, masu bibiyar al'amura a Iran na bayyana Raisi a matsayin wanda zai gaji Shugaban Addinin ƙasar da tsufa ya cim ma. Tun lokacin da yake matashi, Raisi ya samu ilimin addini sosai kasancewar sa aɗlibin Makarantar Qom, Babbar Makaranta a Iran da mafi yawan ta mabiya Shi'a ne.

Fuskantar yaƙe-yaƙe

A ƙarƙashin shugabancinsa, Raisi ya fuskanci tashin hankali daga yaƙin Ukraine, inda ƙarara Tehran ta nuna goyon baya ga Rasha, tana sayar da jiragen yaƙi marasa matuƙa ƙirar Iran ga Moscow, haka a rikicin gaza da ake yi, inda Isra'ila ta zargi babbar maƙiyiyarta da bayar da horo ga mayaƙan Hamas tare da ba su makamai.

A ƙarƙashin mulkin Raisi, Iran ta ci gaba da haɓakawa da sarrafa makamashin Yuraniyom, tana kara fuskantar suka daga Yammacin duniya da Isra'ila a yayin da tsamar da ke tsakanin Tehran da Washington ta ƙaru.

Amurka ta sanya takunkumi ga Raisi saboda kasancewarsa mai shigar da ƙara a yayin shari'ar 1988 mai rikitarwa. Sakamakon haka, ya zama shugaban ƙasar Iran na farko da Amurka ta saka wa takunkumi.

A wani rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya, an bayyana yadda Raisi ya taka rawa a fagen shari'ar Iran da ya amince da a zartar da hukuncin kisa kan yara ƙanana tara a tsakanin 2018 da 2019.

An kuma taso gwamnatin Raisi sosai sakamakon yadda ta tsare Mahs Amini har ya mutu, inda hakan ya janyo zanga-zanga a ƙasar a ƙarshen 2022.

"Ba za a iya bayar da kariya ga abubuwan da ya aikata ba," in ji Karimkhan.

TRT World