Shugaban addinin na Iran ya naɗa Babban Mataimakin Shugaban Ƙasa, Mohammad Mokhber a matsayin sabon shugaban ƙasa, bayan rasuwar Shugaba Ebrahim Raisi a hatsarin jirgi.
Ali Khamenei ya fitar da wannan sanarwa cikin saƙon ta'aziyya da ya yi bayan rasuwar Shugaba Raisi a hatsarin na ranar Lahadi. A ranar Litinin ne aka gano jirgin helikwaftan da ya faɗi a arewa maso yammacin Iran.
A sanarwar, Khamenei ya kuma sanar da kwanaki biyar na makoki cikin saƙon nasa.
Su ma ɓangarorin mulki guda uku na Iran sun gudanar da taro na musamman a Litinin ɗin, inda Mokhber ya wakilci ɓangaren zartarwa, a cewar gidan talabijin na ƙasar.
Mokhber ya ce, "Za mu ci gaba da bin tafarkin Shugaba Raisi wajen sauke nauyi da aka ɗora mana, ba tare da tangarɗa ba".
Madafu uku na mulkin ƙasar da gidan talabijin ɗin ya ambata su ne, ɓangaren zartarwa, da majalisa, da ɓangaren shari'a.
An sanar da rasuwar Ebrahim Raisi, da Ministan Harkokin Waje, Hossein Amirabdollahian, da wasu manyan jami'an gwamnati a safiyar Litinin, bayan kwashe dare ana neman su duk da cikas ɗin yanayi a yankin da abin ya faru.
Tarin tawagogin jami'an agaji ne suka bazama zuwa wani yanki mai tsaunuka a gundumar Gabashin Azerbaijan a arewa maso yammacin Iran, inda hatsarin ya auku da tsakar ranar Lahadi.