Ƙasashen Qatar da  Iraki da kuma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa na daga cikin ƙasashen da suka nuna goyon baya da kuma jajantawa kan rasuwar shugaban Iran Ebrahim Raisi. / Hoto: AFP  

An gano gawawwakin Shugaban Iran Ebrahim Raisi da Ministan Harkokin Wajen Ƙasar da sauran mutane a wurin da wani jirgi mai saukar ungulu ya yi haɗari, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta kasar ta rawaito.

Ko da yake kafar talabijin ɗin kasar ba ta ba da cikakken bayanin kan musabbabin hatsarin jirgin ba a yankin Gabashin iyakar Iran da Azabaiijan.

Raisi ya samu rakiyar Ministan Harkokin Wajen Ƙasar Amirabdollahian tare da gwamnan lardin Azabaijan ta Gabas a Iran da kuma wasu jami'ai da masu gadinsa, a cewar rahoton kamfanin dillacin labaran Iran .

Tun bayan tabbatar da mutuwar Raisi da jami'an gwamnatin Iran suka yi, shugabannin ƙasashen duniya suke ta nuna alhininsu tare da jajanta mutuwar.

Turkiyya ta mika ta'aziyyarta ga Tehran kan rasuwar Raisi da wasu manyan jami'ai a wani haɗarin da ya afku na jirgin sama mai saukar ungulu, Shugaba Erdogan da ministan harkokin wajen kasar sun bayyana cewa,

"Turkiyya tana goyon bayan Iran a wannan mawuyacin lokaci na bakin ciki," in ji Shugaba Erdogan.

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan, shi ma ya jajanta aukuwar lamarin, yana mai cewa ''abin takaici da kuma baƙin ciki ne samun labarin mutuwar shugaba Iran da ministan harkokin wajen ƙasar. Muna cikin jimami da damuwa irin wacce 'yan 'uwanmu na iran ke ciki.''

Jim kadan bayan aukuwar haɗarin a yankin arewa maso yammacin lardin Azarbaijan na kasar Iran a yammacin Lahadi, Turkiyya ta tura da dukkan wasu muhimman kayan aiki da za su taimaka wajen ayyukan bincike da ceto a wurin, in ji shi.

Fidan ya ce, Turkiyya na fatan ''Allah ya jiƙan waɗanda suka rasa rayukansu,'' tare da mika ta'aziyya ga al'ummar Iran.

Firaministan Indiya Narendra Modi ya ce, ya yi matuƙar baƙin ciki da kaɗuwa bisa mummunan labarin mutuwar shugaban Iran Ebrahim Raisi.

"Ina mika ta'aziyyata ga iyalansa da al'ummar Iran." a cewar wani saƙo da Modi ya wallafa a shafin X, yana mai cewa Indiya tana tare da Iran a wannan lokaci na baƙin ciki.

Shi ma Ministan Harkokin Wajen Indiya S Jaishankar ya wallafa a shafinsa na X cewa ya yi ''matukar kaɗuwa da jin labarin rasuwar Raisi da takwaransa Hossein Amirabdollahian.''

“Muna miƙa ta’aziyya ga iyalansu,” in ji shi. "Muna tare da al'ummar Iran."

A cikin wani sakon da ya wallafa a shafin X a ranar Litinin, shi ma Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif ya miƙa ta'aziyyarsa ga "'yan'uwa a Iran" a madadinsa da al'umma da gwamnatin Pakistan baki ɗaya.

"Al'ummar Iran za su shawo kan wannan mumunar tashin hankali cikin juriya da jajircewa," a cewar Sharif.

Pakistan za ta yi zaman makoki na yini guda, kana za a sauke tutar ƙasar rabi a matsayin alamar girmamawa ga shugaban Iran Ebrahim Raisi da sauran wanɗanda suka mutu a hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu, in ji Sharif.

Ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov a cikin wata sanarwa da ya fitar ya bayyana cewa Raisi da Amirabdollahian an san su a mstayin "amintattun aminan gaskiya a ƙasarmu ."

Shugaban kasar China Xi Jinping ya bayyana cewa, mutuwar shugaban Iran Ebrahim Raisi na zama babban rashi ga al'ummar Iran, a cewar sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen China ta fitar

''Shugaba Xi Jinping ya yi nuni da mummunan yanayin mutuwar Shugaba Raisi na zama babban rashi ga al'ummar Iran kana suma al'ummar China sun yi rashin amini,'' a cewar mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen China Wang Wnebin a wani taron manema labarai da aka gudanar.

Lebanon ta sanar da zaman makoki na kwanaki uku a ƙasar saboda mutuwar shugaban Iran da ministan harkokin wajen ƙasar.

Kakakin gwamnatin Japan Yoshimasa Hayashi ya ce Japan na miƙa saƙon ta’aziyya ga gwamnati da jama’ar Iran sakamakon rasuwar shugaba Raisi da ministan harkokin haje.

Shugaban Venezuela Nicolas Maduro a wata sanarwa ta shafin X ya ce “….ya yi matuƙar baƙin ciki da yin bankwana da mutum abin koyi, shugaban da ba a cika samun irin sa ba a duniya wato ɗan uwanmu Ebrahim Raisi, kuma zai ci gaba da kasancewa mutum mai nagarta, mai kare martabar ƙasarsa da al’ummarsa, babban abokin kasarmu.

"Daga nan kasarmu, muna miƙa sakon ta’aziyya ga Shugaban Addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei da ‘yan uwa maza da mata da ke Iran.”

Sarkin Qatar Shaikh Tamim bin Hamad al Thani ya aike da sakon ta’aziyya ga gwamnati da jama’ar Iran sakamakon rasuwar shugaba Raisi.

Firaministan Iraki Mohamed Shia al Sudani a wata sanarwa da ya fitar ya bayyana goyon bayan Iraki ga al’ummar Iran da shugabanninta a wannan lokaci na rintsi.

Shugaban Masar Abdul Fatah al Sisi ma ya fitar da sanarwa inda ya ce “Shugaban Jumhuriyar Larabawa ta Masar na mika tsantsar ta’aziyya da jimami ga ‘yan uwa jama’ar Iran.” Ya kuma ce Jumhuriyar Larabawan Masar na tare da shugabanni da jama’ar Iran a wannan mawuyacin hali.

Shugaban Sri Lanka Ranil Wickremesinghe ya fitar da sanarwa ta shafin X cewa “Ina miƙa saƙon ta’aziyya da jimamina ga iyalan waaɗnda suka mutu da gwamnati da jama’ar Iran. Addu’o’i da zukatanmu na tare da iyalan Raisi da na ‘yan tawagarsa.”

Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa Shaikh Mohamed bin Zayed al Nahyan ma ya aika da saƙon ta’aziyya ga gwamnati da jama’ar Iran sakamakon rasuwar shugaban Iran da Ministan Harkokin Waje, yana mai cewa kasarsa na tare da Iran a wannan lokaci mai tsanani.

Sarkin Jordan Abdullah ya fitar da sanarwa ta shafin X cewa “Ina mika tsantsar ta’aziyya ga ‘yan uwa da shugabanni da gwamnatin Jumhuriyar Musulunci ta Iran bisa rasuwar Dan Uwa Shugaba Ebrahim Raisi da Ministan Harkokin Waje Dan Uwa Hossein Amirabdullahian da ‘yan tawagarsu, Allah ya gafarta musu baki ɗaya. Muna tare da jama’ar Iran a wannan lokaci na rintsi da wahala.”

Firaministan Malaysia Anwar Ibrahim a wata sanarwa da ya fitar ta shafin sada zumunta na yanar gizo ya ce ya yi “matukar baƙin ciki” da rasuwar shugaban Iran Ebrahim Raisi da sauran jami’an gwamnati a hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu.

TRT World