Bayan binciken da aka kwashe tsawon dare ana yi sakamakon rashin kyawun yanayi, a yanzu an tabbatar da rasuwar shugaban Iran Ebrahim Raisi, da ministan harkokin waje, Hossein Amirabdollahian, da wasu manyan jami'an ƙasar.
Tarin tawagogin jami'an agaji ne suka bazama zuwa wani yanki mai tsaunuka a gundumar Gabashin Azerbaijan a arewa maso yammacin Iran, inda hatsarin ya auku ranar Lahadi.
Bisa tsarin mulkin ƙasar, babban mataimakin shugaban ƙasa, Mohammad Mokhber, shi ne zai karɓi mulki yanzu a matsayin sabon shugaban ƙasar na tsawon kwanaki 50.
Daga yanzu zuwa lokacin, wata babbar majalisa da ta ƙunshi babban mataimakin shugaban ƙasa, da kakakin majalisar dokoki, da shugaban ɓangaren shari'a za su tabbatar an gudanar da zaɓe.
Ayar doka ta 131 ta tsarin mulkin Iran ce ta ce, a yayin rasuwa ko rashin lafiyar shugaba mai ci.
"Idan aka samu rasuwa, cirewa, murabus, ko rashin lafiyar shugaban ƙasa na tsawon watanni biyu, ko idan aka samu ƙarewar wa'adin mulki kuma ba a zaɓi sabon shugaban ƙasa ba saboda matsaloli, babban mataimakin shugaban ƙasa zai karɓi mulki tare da amincewa shugabanni, da majalisar da ta ƙunshi kakakin majalisa, da shugaban ɓangaren shari'a, kuma babban mataimakin shugaban ƙasa ya wajaba ya shirya zaɓen shugaban ƙasa na wuri cikin kwanaki hamsin a maƙura," cewar ayar dokar.
An zaɓi Raisi a matsayin shugaban ƙasa a 2021 bayan ya lashe zaɓe da gagarumin rinjaye, inda ya samu ƙuri'u miliyan 17.9 daga cikin miliyan 28.9 da aka kaɗa a zaɓen.
A baya ya riƙe muƙamin shugaban ɓangaren shari'a, sannan ya riƙe shugabancin Hubbaren Imam Reza a birnin Mashhad, inda nan ne asalin Raisi.